Kamfanin dilalncin labaran iqna ya
habarta cewa, ya nakalto daga tashar talabijin ta Press TV ta bayar da rahoton
cewa, kungiyar Hizbullah ta bayyana wannan mataki da cewa abin takaici ne,
domin bai kamata kasar larabawa kamar Masar ta zama tana aiwatar da irin
wadannan manufofi na Isra'ila ba.
Bayanin ya ce mene ne abin da mahukuntan larabawa suke tsoro ne daga tashar Almanar, alhali ita babban abin da ta saka a gaba shi ne bayani kan zaluncin yahudawan Isra'ila a kan al'ummar musulmi na palastinu, kamar yadda kuma take fallasa duk wani makirci da ake kitsa wa kasashen musulmi.
Kungiyar Hizbullah ta ce tana yin kira ga mahukuntan kasar Masar da su sake yin nazari dangane da wannan mataki da suka dauka, domin kuwa yin hakan ba maslaha ce gare su ba, maslaha ce ga yahudawa da kuma karnukan farautarsu da ke yankin.
Kamfanin Nilesat na gwamnatin Masar bayan yanke tashar talabijin ta Almanar mallakin kungiyar Hizbulla da ke watsa shirinta daga Lebanon, haka nan kuma kamfanin na shirin yanke wasu tashoshin na Lebanon, da suka hada da Aljadid, NBN, MTV, Lebanon TV, saboda dalilai na siyasa, musamman ma fallasa larabawa masu daukar nauyin ayyukan ta'addanci da suke yi, da kuma bayar da cikakken bayani kan kisan gillar da Saudiyya ke yi akn fararen hula a Yemen.
Tun kafin wannan lokacin dai kamfanin tauraron dan adam na Arabsat ne ya fara yanke tashar Almanar, wanda kuma kamfanin mallakin gwamnatin Saudiyya ne da yake da ofishi a birnin Amman na kasar Jordan.