IQNA

Wata Daliba Musulma A Amurka Ta Byayana Yadda Ake Kyamar Musulmi

23:44 - April 14, 2016
Lambar Labari: 3480322
Bangaren kasa da kasa, Su’ad Al-bahwati wata daliba musulma a makarantar Hill da ke jahar Peselvania ta bayyana yadda take fuskantar matsalar kyama a halin yanzu a Amurka.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Reading Eagle cewa, Su’ad Al-bahwatita ce tun daga lokacin da ta fara saka cikakken hijabin muslunci ta fuskanci matsaloli da dama.

Ta ci gaba da cewa babbar matsalar da take fuskanta it ace yadda ake nuna mata kyama da rashin aminci, saboda ahaka a kowane lokaci ta fit aba ta jin cewa tana cikin aminci har ta dawo zuwa gidansu.

Baya ga haka kuma wata matsalar it ace, hatta a cikin makaranta inda take tare da kawanyenta yan jinsu da ma sauran dalibai wadanda suke tare da jimawa sun santa ta sansu, amma saboda saka hijabi yanzu ta zama saniyar ware.

Kamar yadda kuma wannan matsala ba ta takaita da makaranta ba kawai, matsala ce ta rayuwa baki daya, alhali kuma ita tana yin hakan ne domin shi ne koyarwar manzon Allah (SAW) ga mata musulmi.

Su’ad ta ce hakan baya rasa nasaba ne da abin da yake faruwa a duniya a halin yanzu na ta’addanci, inda wasu suke amfani da sunan addinin musulunci wajen aikata muggan laifuka na kisan bil adama da sunan jihadi.

Ta ce ko shakka babu wanan ya bar mummuna tasiri a cikin kwakwalen muatne turai dangane da addinin muslnci,inda da dama suke kallon musulmi a matsayin yan ta’adda.

Sai a cewarta ba duka a aka taru aka zama day aba, wadanda su kuma sabain haka suke, basu irin wannan mahanga kan musulmi, bil hasali ba idan suka fahimci cewa mace musulma ce suna karrama ta tare da kokarin ganin sun kare mutuncinta daga masu hankoron tozarta ta.

3488556

captcha