Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hlda da jama’a na babbar ciobiyar yada al’adun muslunci ta Iran cewa, an gudanar da tattanawa tsakanin karamin jadan Iran a Kampala Ali Bakhtiyari da kuma babban mai bayar da fatawa Ugdanda Sheikh Diranguwa.
Bayanin yace bangarorin sun cimma matasa kan yin aiki tare a bangarori da suka shafi kada bunkasa harkokin da suka danganci kur’ani mai tsarki.
Daga cikin muhimman abubwa da da za su kara mayar da hankali kuwa aknsu akwai batun shirya bayar da horo ga musulmi na kasar kan ilmomin kur’ani mai tsarki.
Daga ciki kuwa har da karatu da kuma harda, gami da sauran bangarori na ilmomin kur’ani da ya kamata musulmi su kara saninsu yadda ya kamata domin sanin umarnin Allah da hanninsa, da kuma sanin ilmomin wannan littafi mai girma.
Babban mai bayar da fatawa kasar ta Uganda Sheikh Diranguwa ya bayyanacewa, sun yi murnna matuka da wannan fahimtar juna da aka samu a tsakaninsu da Iran, kasar da ya ce tana taka gagarumar rawa wajen ci gaban al’ummar musulmi na duniya baki daya.
A nasa bangaren karamin jakadan kasar Iran a kasar ta Uganda Ali Bakhtiyari ya bayyana cewa, kasarsa tan akokari domin ganin an samu hadin kai a tsakanin dukaknin al’ummar msuulmi ba tare da wani bananci ba.
Ya kara da cewa samun hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi, shi ne babban mabudin samun nasara gare su a cikin dukkanin lamrra da ska saka agaba a matsayi na duniya da kuma lahira.
Haka nan kma wannan zai ba su damar zama hadaddiyar al’umma guda mai karfi.