IQNA

Jagoran Juyi:

Tarbiyantar Da Matasa Kan Manufofin Juyi Shi Ne Hanyar Yakin Kwakwalwa

23:45 - April 20, 2016
Lambar Labari: 3480342
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan membobin kungiyar hadin kan daliban makarantu ta Iran inda ya bayyana cewar daya daga cikin fagagen da aka shata daga tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ma'abota girman kan duniya shi ne fagen matasa

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewam a lokacin da yake ganawa da daliban ya bayyana cewa: Masu fada da tsarin Jamhuriyar Musulunci suna kokari ne wajen sauya tunani na addini da juyin juya hali na matasan Iran, kawar da irin fata mai kyau da suke da shi bugu da kari kan kazar-kazar din da suke da shi. A saboda haka babbar hanyar fada da wannan makirci mai sarkakiya ita ce tarbiyyar matasa bisa tafarki na addini da koyarwar juyin juya hali, tsarkin zuciya, yin taka tsantsan, kyakkyawan fata, jaruntaka da sadaukarwa.


Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fara jawabinsa ne a yayin wannan ganawar da kiran matasan zuwa ga amfanuwa da irin damar da ke cikin watan Rajab sannan kuma da watan Sha'aban da Ramadhan inda ya ce: Wadannan watanni guda uku watanni ne na karfafa ruhi. A saboda haka matasa wadanda suke cikin samartakarsu za su iya amfanuwa da wannan dama wajen karfafa ruhinsu.

Daga nan kuma sai Ayatullah Khamenei ya ci gaba da karin haske kan wasu fagage da ake samun kace nace tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ma'abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka da sahyoniyawan duniya inda ya ce: 'Yancin kan kasa da suka hada da 'yancin kai na siyasa, tattalin arziki da al'adu daya ne daga cikin irin wadannan fagage, don kuwa manyan kasashen duniya suna fada ne da duk wata kasa da take fada da mulkin mallakan 'yan kasashen da kuma kare 'yancin kanta.

Jagoran ya bayyana ci gaba a matsayin daya daga cikin fagagen da ake rikici tsakanin tsarin Jamhuriyar Musulunci da ma'abota girman kan inda ya ce: Manyan kasashen duniya dai suna fada da duk wata kasa da take son samun ci gaban kanta ba tare da dogaro da su ba. Don kuwa irin wannan ci gaban zai iya zama abin koyi ne ga sauran kasashe da al'ummomi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar hakan shi ne babban dalilin da ya sanya ma'abota girman kan duniya suka shata daga wajen fada da Iran don hana ta samun wannan kwarewar da kuma fasahar nukiliya da take da shi. Daga nan sai ya ce: Matukar muka nuna gazawa a gaban wadannan masu tinkaho da karfi, to kuwa adawarsu za ta ci gaba har zuwa ga sauran bangarorin ci gaba da suka hada da fasahar ilimin halittu, Nano da sauran bangarori na ilimi masu muhimmanci da sarkakiya. Don kuwa suna adawa da duk wani ci gaba na ilimi, tattalin arziki da wayewa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta samu.

Ayatullah Khamenei ya bayyana tasirin da Iran take da shi a yankin yammacin Asiya da ma duniya ba ki daya, batun Palastinu, gwagwarmaya da kuma tsarin rayuwa ta Iran a matsayin wani fagen da ma'abota girman kai suke da sabani da tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya ce: matukar irin tsarin rayuwa ta yammaci ta sami gindin zama a wata kasa, to kuwa masana da masu fadi a ji na wannan kasar za su zamanto masu mika kai ne ga siyasar ma'abota girman kai.

Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana batun matasa a matsayin daya daga cikin manyan fagagen da ake da sabani tsakanin Iran da manyan kasashen duniyan inda ya ce: A halin yanzu dai akwai wani rikici da fito na fito da ke gudana tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bangare guda da kuma Amurka da sahyoniyawa a bangare guda.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana matasa daliban makarantun sakandare da na jami'oi a matsayin sojojin wannan fito na fiton inda ya ce: A fagen wannan yakin dai ana iya ganin wasu nau'oi biyu na dakaru sannan kuma masu akidu mabambanta, wanda sakamakon yakin ya danganta ne da irin yanayi da tsarin wadannan sojoji biyun.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar irin wannan yakin ya fi yaki na makami hatsari, don haka yayin da yake ishara da wasu makirce-makircen makiya a wannan bangaren ya bayyana cewar: A wasu lokuta suna mana barazana da yaki da kawo hare-hare da ruwan bama-bamai. Wannan wata magana ce ta wauta da kuskure. Don kuwa ba su da karfi da kuma jaruntakar yin hakan. Amma idan har ma suka yi hakan, to kuwa za su debi kashinsu a hannu.

Haka nan kuma yayin da yake maganar cewa a halin yanzu ma makiyan suna ci gaba da yaki na kwakwalwa a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda kuma maimakon kariya ya kamata a ce ana mayar da martani ma, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Matukar dai muna da dakaru ma'abota riko da addini da koyarwar juyin juya halin Musulunci sannan kuma ma'abota tunani da jaruntaka da sadaukar da kai a fagagen dagan mu, to kuwa za a iya kirdadon sakamakon wannan yakin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: To amma matukar dai dakarun mu suka zamanto masu mika kai da fadawa tarkon yaudara, masu yarda da sakin fuskar makiya, marasa laka a jika da tunani da kuma dogaro da kai da sauransu, to kuwa sakamakon yakin a fili yake.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A saboda haka a yayin wannan yaki na kwakwalwa, ana iya samun sojoji masu yanayi biyu; wani soja wanda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta amince da shi da kuma wani sojan wanda ma'abota girman kai suka amince da shi. Kowane guda daga cikin wadannan sojoji yana iya taka rawa wajen tsara sakamakon yakin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Kasashen yammaci musamman Amurkawa suna kokari ne wajen mayar da matasan Iran su zama wasu matasa marasa imani, marasa jaruntaka, marasa laka a jika, marasa kyakkyawar fata da kuma dogaro da makiya, to amma tsarin Musulunci yana kokari ne wajen tarbiyyantar da matasa wajen zama kishiryar abin da ma'abota girman kai suke son su zama.

Don haka sai yayi kira zuwa ga kula da kuma ba wa matasan tarbiyyar da ta dace, kamar yadda kuma ya kirayi jami'an ma'aikatun ilimi da tarbiyya ta kasar Iran da su sauke nauyin da ke wuyansu a wannan bangaren.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yanayin da matasan kasar Iran suke ciki a matsayin yanayi da ke cike da fata mai kyau inda ya ce: Duk kuwa da wasu abubuwa da ake da su masu kautar da matasa daga kan tafarki madaidaici bugu da kari kan irin fagage na kiyayya da ake yiu da su, to amma a halin yanzu muna da matasa ma'abota imani, masu kusaci da Ubangiji, masu tattaki ranar arba'in, ma'abota karatun Alkur'ani, I'itikafi kana kuma ma'abota tsayin daka a fagage daban daban na juyin juya halin Musulunci, wanda abin godiya ce ga Allah Madaukakin Sarki.

Ayatullah Khamenei ya bayyana samuwar irin wadannan matasan a kasar Iran a matsayin wani lamari mai girman gaske. Har ila yau kuma yayin da yake jaddada cewa bayan shekaru 37, har ya zuwa yanzu ma'abota girman kai sun gagara kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ko kuma su hana ta ci gaba, Jagoran ya bayyana cewar: Duk da barazana a aikace da kuma farfagandar da ake yadawa, amma a halin yanzu kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta tabbatar da matsayinta a duniyar musulmi. A saboda haka yin Allah dai da ita da wata lalatacciyar gwamnati ‘yan amshin shata wacce aka bar ta a baya, ba shi da wani muhimmanci.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da shan kashin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta sha a yakin kwanaki 33 da kuma kwatanta irin wannan nasarar da shan kashin da sojojin kasashen larabawa uku a gaban sojojin haramtacciyar kasar Isra'ilan, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Kungiyar Hizbullah da matasanta muminai, har ya zuwa yanzu suna ci gaba da haske tamkar hasken rana sannan kuma sun zamanto abin alfaharin duniyar musulmi.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne gaskiya ta fuskanci matsaloli da wahalhalu, to amma daga karshe dai za ta yi nasara.

Ayatullah Khamenei ya bayyana tsayin dakan dakarun gaskiya a matsayin sharadin na asali na nasarar gaskiya a kan karya inda ya ce: Gaskiya da hakika tana tare da wadannan matasan, kuma da yardar Allah wata rana za ta zo da matsalolin da ake fuskanta za su kawu, sannan kuma wadannan matasan za su kasance a sama.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci sai da wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kungiyar hadin kan daliban Musulunci Hujjatul Islam wal muslimin Hajj Ali Akbari ya gabatar da jawabinsa dangane da ayyukan da kungiyar ta ke yi wajen tarbiyyar daliban makarantu.

Har ila yau kuma wasu dalibai biyu daga cikin membobin kungiyar su ma sun gabatar da jawabinsu inda suka yi Karin haske dangane da irin matsaloli da kalubalen da suke fuskanta.

3490558

captcha