IQNA

An Zargi Sojojin Nijeriya Da Tafka Ta'asar Kisan ‘Yan Shi’a

23:41 - April 22, 2016
Lambar Labari: 3480346
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da yin kisan gilla kan mabiya mazhabar shi’a a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakakto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da yin kisan gilla kan mabiya mazhabar shi’a a cikin watan Disamban 2015.

Kungiyar kare hakkokin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta zargi rundunar sojin Najeriya da yin rufa-rufa game da kisan kiyashin da suka yi wa 'yan kungiyar Harkar Musulmi ta mabiya tafarkin Shi'a a kasar a shekarar da ta gabata.

Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani sabon rahoton da ta fitar inda suka ce wasu shaidun gani da ido sun bayyana musu yadda sojojin Nijeriya suke kona gawawwakin mutane da ransu.

Har ila yau Kungiyar Amnesty International cikin rahoton na ta ta zargin sojojin da wanke jinin da ya zuba a kan tituna bugu da kari kan kwashe harsasan da suka yi amfani da su wajen kashe 'yan kungiyar Islamic Movement din , kamar yadda kuma suka rushe gidajen da suka aiwatar da kashe-kashe domin rufe duk wata shaida da za a iya amfani da ita wajen tabbatar da zargin da ake musu na kisan kiyashin.

Rundunar sojin ta Nijeriya dai ta musanta irin wadannan zarge-zarge da ake mata tana mai musanta adadin mutanen da aka ce sun kashe din, to sai dai kuma a kwanakin baya babban sakataren gwamantin jihar Kaduna ya tabbatar da cewa sojojin sun ba su gawawwakin 'yan kungiyar IMN din su 347 da suka kashe kana kuma suka bisne su a manya-manyan ramuka lamarin da ke karyata ikirarin sojojin.

Sojojin Nijeriyan dai sun zargi 'yan kungiyar 'yan'uwa musulmin karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzky da kokarin kashe babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Yusuf Buratai ne a lokacin wata ziyara da ya kai Zaria, lamarin da 'yan kungiyar suka musanta.

3490921

captcha