IQNA

An Kwadaitar Da Musulmi Da Su Rika Gina Masallatai A Najeriya

23:19 - May 04, 2016
Lambar Labari: 3480383
Bangaren kasa da kasa, Abdullatif Abdulhakim jami’I a ma’aikatar kula da da harkokin gine-gine a jahar Lagos ya kwadaitar da musulmi kan gina masallatai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Jaridar Daily Trust cewa, Abdulhakim ya bayyana masallaci a mtsayin wurin ayyukan al’ad da siasa da zamantakewa, ba wurin ibada ba kawai.

Ya ci gaba da cewa hakika masllaci wuri ne da mutane da dama suka dauka cewa ya kebantu da salla ne kawai, alhali wuri ne wanda ake gudanar da harkokin koyar da ilimi da karfafa ruhi da warware battuwa na zamantakewa da siyasa ta muslmi.

Haka nan kuma nan cibiya ta taruwa muuslmia kowane lokaci domin jin abin da ya rataya a kansu a fuskar koyarwar addini, amma a cewarsa wasu suna gina gidaje manya, amma bas u kula da gina masallatai yadda ya kamata, ko kuma ba su yi ma sam.

Ya jadda cewa wajibi ne da ya rataya kan musulmi baki daya da su raya sha’anin masallatai da gina su da kuma kula da su.

3494947

captcha