
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jaridar Guardian cewa, Sadiq Khan dan shekaru 45 a duniya ya lashe zaben Magajin garin London a karkashin babbar jam'iyyar adawar Biritaniya ta Labour.
Jin kada bayan lashe zaben shugaban jam'iyyar Labour, Jeremy Corbyn ya aike da sakon taya murna ta shafin sa twitter, ga Sadiq Khan, yana mai cewa ''ina mai jiran ganin na fara aiki tare da kai domin maida London gari na kowa da kowa''
Wannan sakamakon zaben dai zai kara wa shugaban jam'iyyar Labour, Jeremy Corbyn kwarin-gwiwa.
Tun da farko dai wasu sunyi hasashen cewa jam'iyyar za ta yi mummunar faduwa kasancewar koma bayan data fuskanta a wasu sassan kasar a yayin zaben jihohi dana kananan hukumomi na ran Alhamis data gabata.
Mayan ayukan dake gaban sabon magajin garin na Londan sun hada da magance matsalar tsadar gidaje, sifiri, da kuma gurbatar yanayi
Shi dai wannan musulmi na farko da ya kasance Magajin garin Landan karkashin babbar jam'iyar adawar Burtaniya ta Labour, Sadiq Khan ya sha rantsuwar fara aiki.
a wani biki a Southwark Cathedral dake birnin, Mr Khan dan wani direban bus dan cirani daga kasar Pakistan, ya ce yana zai wakilici ko wane bangare da al'ummar birnin.
Ya ce burinsa shine ya tabbatar da cewa daukacin mazauna birnin Landan sun samu damar da ya kamata ya samu.
Galabar da ya samu kan dan attajirnin nan takarar jam'iyar Conservative, Zac Goldsmith, na nuni da dawowar mulkin jam'iyar Labour a birnin na Landan, bayan shekaru takwas.
Sakamakon zaben dai zai kara wa shugaban jam'iyyar Labour, Jeremy Corbyn kwarin-gwiwa.
A baya dai jam'iyyar tasu ta fuskanci koma-baya a wasu zabukan da aka gudanar a kasar.
Sai dai jam'iyyar ta ba wa marada kunya dangane da hasashen da wasu ke yi cewa za ta yi mummunar faduwa a Ingila.