Kamfanin
dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na
Palastinu cewa, yahudawan sahyniya suna ci gaba da keta alfarmar masallacin
Aqsa mai alfarma, da suna cewa suna ibada.
Bayanin ya ci gaba da cewa tyahdawan suna yin hakan ne bias hujjoji daban-daban, tare da samun cikakken goyon baya da dauki da kuma kariya daga jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila.
Yahudawan sahyniya mazauna wani matsugunnin yahudawa yan share wuri zauna a kusa da birnin ne suka shiga cikin masallacin mai alfama, da sunan za su ziyarci Haikal Sulaiman.
Bisa wannan karya da suke rayawa dangane da batun a bin da suke kira Haikal Sulaiman da ke cikin malassaci, wannan ya sanya suna keta alfarmar wannan wuri mai tasarki a duk lokacin da suka ga dam aba tare da wani ya isa ya iya taka musu birki ba.
Masu tsatsauran ra’ayi daga cikin yahdawan sahyuniya ne deai suke aikata irin wannan aika aika, inda suke shiga wurin domin cin zarafin musulmi masu salla a cikinsa a duk lokacin da suka bushi iskan yin hakan.