IQNA

Jami’ar Amurka Za Ta Dauki Nauyin Taro Tsakanin Musulmi Da kirista

20:51 - May 12, 2016
Lambar Labari: 3480406
Bangaren kasaa da kasa, ana shirin gudanar da wani zaman taro na kara kusanto da fahimta a tsakanin mabiya addiin muslunci da kuma kiristanci a jami’ar Cent Joseph da ke Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Baffalo News cewa, Shahnaz Bat tsohuwar shugabar kungiyar musulmi mata akasar Amurka ta bayyana cewa, idan aka yi la’akari da abin da ke cikin kur’ani yana ishara da Maryam (AS)

Ta ce ko shakka babu muslunci yana girmama Maryam (AS) da kuma danta annabi Isa (AS), idan aka yi la’akari da yadda muslunci yake girmama su to za a fahimci cewa ba shi da wata husuma da wani addini.

A wannan zaman taron dai an asamn halartar mabiya addinan kirista da kuma na muslunci, inda ake gabatar da jawabai na hadin kai da fahimtar juna atsakaninsu.

Musulmin kasar dai suna fuskantar matsaloli tun bayan da yabn ta’adda suka fara kaddamar da hare-hare da sunan addinin muslunci, wadanda suke dauke da akidar ta’addanci.

3497319

captcha