IQNA

Jagora Juyi:

Tsayin Dakan Malamai Da Al’umma Ne Yasa Juyin Islama Yake Ci Gaba Da Wanzuwa

23:48 - May 15, 2016
Lambar Labari: 3480413
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a lokacin da yake ganawa da shugabannin da malamai na makarantun addinin muslunci na Tehran ya bayyan acewa, tsayin dakan da malamai tare da al’umma suka yi ne ya sanya juyin Islama yake ci gaba da wanzuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin jagora na yana gizo cewa, a safiyar yau Asabar (14-05-2016) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da manyan jami'ai, malamai da daliban makarantun hauzozin birnin Tehran, inda ya bayyana ‘shiryarwa ta tunani da addini' da ‘shiryarwa ta siyasa da amfani da basira' da kuma ‘hannunka mai sanda da kasantuwa a fagagen hidimar al'umma' a matsayin wasu nauyi masu girma da suke wuyan malaman addini. Daga nan sai ya ce: Wajibi ne dalibai ta hanyar sama wa kansu dacewa da fahimtar da ake bukata, su shirya kansu wajen sauke nauyin da ke wuyansu a cikin al'umma.

Haka nan kuma yayin da yake kiran daliban zuwa ga girmama wannan dama ta dalibta da suka samu, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Koda an sami dukkanin kwarewar da ake bukata a cikin wata al'umma, to amma sai ya zamanto wannan al'ummar ba ruwanta da addini, to kuwa wannan al'umma a rayuwarta ta duniya da lahira za ta fuskanci hasarori da matsaloli na hakika. Wannan gagarumin nauyin kuwa, wato nauyin mayar da wata al'umma zuwa ga al'umma ma'abociyar addini, wani nauyi ne da ke wuyan malamai da daliban addini.

Jagoran ya bayyana ma'anar shiriya ta addini a matsayin bayanin koyarwa da tunani na Musulunci na hakika. Sannan kuma yayin da yake magana kan irin tasirin da kafafen watsa labarai na zamani musamman internet suke da shi wajen kara irin shubuhohin da ake shigowa da su kan addini da kuma manufar da wasu suke da su na shigo da gurbatattu da munanan tunani cikin kwakwalan matasa, Jagoran ya bayyana cewar: Hakikan wannan wani fage ne na yaki na hakika. Don haka wajibi ne malamai da daliban makarantun addini su zamanto cikin shiri da kwarewar da ake bukata wajen shiga wannan fage na fada da irin wadannan shubuhohi da gurbatattun tunani da koyarwar da ake shigowa da su.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana ‘Musuluncin da aka bar shi a baya wanda babu fahimta na hakika a tattare da shi' a matsayin misali na hakika na irin wadannan karkatattun tunani yana mai cewa: a daya bangaren kuma shi ne ‘Musulunci samfurin Amurka' wanda yake fada da ‘Musulunci na hakika'.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana ‘fahimtar Musulunci na hakika wanda ya dogara da Alkur'ani da Sunna' ta hanyar amfani da tunani da hikima ta Musulunci a matsayin babban aikin malamai, daga nan sai ya ce: Tafarkin annabawa shi ne yada irin wannan tunani na asali. Malamai kuwa su ne masu ci gaba da riko da kuma yada wannan tafarki da ke cike da sa'ada, wato masu shiryar da mutane a bisa tafarkin addini.

Jagoran ya bayyana shiryar da mutane a aikace a matsayin mai kammala shiryar da tunaninsu yana mai cewa: Ku yi kokari wajen shiryar da mutane ta mafi kyawun hanya zuwa ga ibada, riko da koyarwar addini na zahiri ciki kuwa har da gaskiya, rikon amana, tsoron Allah, barin sabo, umurni da kyawawan halaye da kuma ingantacciyar rayuwa.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne ta hanyar dogaro da ingantattun dalilai ku yi kokari wajen dawo da akidun mutane wadanda watakila saboda gushewar shekaru su yi rauni zuwa ga ingantaccen tafarki.

Ayatullah Khamenei ya bayyana "shiryarwa ta siyasa" a matsayin wani nauyi mai muhimmanci da ke wuyan malamai inda ya ce: Dalilin da ya sanya na ke yawan magana kan wajibcin tabbatar da tunani na juyin juya hali a makarantun hauza shi ne cewa tabbatar da ci gaba da tafiya bisa tafarkin juyin juya hali ba abu ne mai yiyuwa ba, in ba tare da kasantuwar malamai ba.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da batun "haramcin shan taba (da malamai suka fitar), da yunkurin kare kundin tsarin mulki da yunkurin ‘yan kasantar da kamfanonin man fetur na Iran" Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Yunkurin kare kundin tsarin mulki da ‘yan kasantar da kamfanonin man fetur don fuskanci matsaloli da rashin kai wa ga gaci ne sakamakon rashin kasantuwar malamai a cikinsu ne. To amma hikimar marigayi Imam Khumaini (r.a) shi ne cewa bai bari makiya sun kawar da tasirin malamai a cikin yunkurin juyin juya halin Musulunci da kuma bayan nasararsa ba. Don kuwa idan har da hakan ta faru, to da kuwa da juyin juya halin Musuluncin bai yi nasara ba, sannan kuma da Jamhuriyar Musulunci ba ta ci gaba da bin tafarkin da take kai ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Amurkawa, tun farko-farkon juyin juya halin Musulunci, kamar yadda a halin yanzu ma suke yi, babban kokarinsu shi ne kawar da malamai daga cikin rayuwa da yunkurin al'ummar Iran, don daga baya su sami damar kamar da kasantuwar mutane a fage, kana daga karshe su sami nasarar kawar da juyin juya halin Musuluncin. To amma har ya zuwa yanzu sun gagara cimma wannan manufa ta su, da yardar Allah a nan gaba ma ba za su yi nasara ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A yayin gagarumar farkawa ta Musulunci da ke faruwa ma, addini shi ne abin da ya janyo mutane shigowa fage. To amma sakamakon rarrabuwan kan cibiyoyin addini a wadannan kasashe hakan ne ya sanya farkawar ba ta kai ga manufar da ake so ba. To amma a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ci gaba da kasantuwar malamai a fage ne ya sanya mutane suka ci gaba da ksantuwa a fagen sannan kuma yunkurin juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da wanzuwa.

Bayan Karin bayani dangane da shiryarwa ta addini da ta siyasa, sai Ayatullah Khamenei ya koma ga nauyi na uku mai muhimmanci da ke wuyan malaman, wato "shiryarwa da kuma kasantuwa a fagen hidima wa al'umma.

Jagoran ya bayyana cewar: Shigowar dalibai fagen yin hidima wa al'umma, gina makarantu, gina asibitoci, taimakon mutane a lokacin faruwar bala'oi da sauran ayyuka, lamurra ne da za su shigo da mutane fage da kuma yi musu hidima.

Haka nan kuma yayin da ya ke kiran daliban zuwa ga ba da himma wajen karatu da tsarkake zukatansu, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Ku ba da dukkanin himmarku wajen sauke nauyinku na malanta wanda babu wani abin da zai maye gurbin hakan. Ko da yake bai kamata a yi mummunar fahimta wa wannan lamarin ba, face dai wajibi ne dukkanin abin da za ku yi ya zamanto don neman yardar Allah Madaukakin Sarki da Imam al-Asr (rayukanmu su zamanto fansa a gare shi) ne.

A wani bangaren na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wasu abubuwan da malamai da daliban makarantun hauzar suka yi ishara da su a jawaban da suka gabatar inda ya ce: Ku yi kokari wajen ganin salon makarantun hauza bai koma zuwa ga salo irin na jami'oi ba. Haka nan kuma tsarin koyar da kyawawan halaye a makarantun hauza da kuma daukan dalibai bayan gudanar da binciken da ya kamata wani nauyi ne da ke wuyan jami'an hauzar.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da muhimmancin makarantar hauzar Tehran da kuma manyan malamai da daliban da suke wajen, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Har ya zuwa yanzu makarantar hauzar Tehran tana da matsayi mai girma. A saboda haka wajibi ne a girmama wannan matsayin don ci gaba da karfafa bangarorin fikihu da sauran darussa da tafsirin Alkur'ani da hadisai.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da Hujjatul Islam wal muslimin Sadiqi Rashad, shugaban majalisar makarantun hauzar lardin Tehran ya gabatar da jawabinsa inda yayi Karin haske kan irin ayyukan makarantar hauzar ta Tehran da irin rawar da ta taka.

Bayan nan kuma wasu daga cikin malamai da daliban makarantun hauzar ta Tehran suka gabatar da jawabansu da bayyana mahangarsu kan baturuwa daban-daban.

Daga karshe dai, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci mahalarta taron sallolin azahar da la'asar.

3497842

captcha