IQNA

Sheikhul Azhar Zai Gana da Pop Francis

22:00 - May 23, 2016
Lambar Labari: 3480440
Bangaren kasa da kasa, a babban malain cibiyar Azhar zai gana da jagoran mabiya darikar katolika a pop Francis a fadar Vatican.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na Sky News Arabis cewa, a karon farko wadannan manyan mutane biyu masu matsayi na adini za su gana da juna.

A wannan ganawa ta su za a duba batutuwa da suke da alaka da batun sulhu da fahimtar juna a tsakanin addinai.

Cibiyar Azahar ta sanar da cewa, bayan ganawa da Pop Francis a yau tare da babban malamin cibiyar, mataimakinsa Abbas Shoman zai jagoranci wata tawaga da za ta tattauna da wani babban malami na majami’ar John Lui Toran, wanda shi ne shugaban majalisar shawara ta Vatican baki daya.

Rafiq Juraish shugaban majami’oin kasar Masar baki daya ya bayyana cewa, shugabannin addinain biyu za su tattauna kuma za su yi musayar ra’ayi kan batutuwa da dama da suka shafi alaka tsakanin bangarorin biyu.

A daya bangaren kuma majami’ar Katolika akasar Masar ta nuna jin dadi da gamsuwa da wannan ziyara ta Ahmad tayyib a fadar Vatican da kuma ganawa da jagoranta, inda suke kallon hakan a matsayin wani lamari na tarihi.

3500453

captcha