IQNA

Ganawar Jagora Da Firayi Ministan India

Mai Da Gas Yaki Da Ta’addanci Chabahar Manyan Bangarorin Aalaka Iran Da India

21:32 - May 25, 2016
Lambar Labari: 3480448
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a ganawar da ya yi da Firayi ministan India ya bayyana cewa akwai alaka mai tsohon tarihi a tsakanin kasashen biyu kuma za ta ci gaba a dukkanin bangarori na tattalin arziki da siyasa da sauransu.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagora cewa, a yammacin yau Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da firayi ministan kasar Indiya Narendra Modi da ‘yan tawagarsa da suka kai masa ziyara, inda yayin da yake ishara da tsohuwar alaka ta al'adu, tattalin arziki da zamantakewa tsakanin Iran da Indiya, ya bayyana cewar fagage da kasashen biyu za su iya aiki tare suna da yawan gaske, don haka sai ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai tana maraba da fadada alaka da kasar Iran wacce tana daga cikin kasashen da tattalin arzikinsu yake ci gaba da fadada da kuma samun ci gaba a duniya, sannan kuma a shirye take wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin kasashen biyu ba tare da barin wata siyasa ta yi tasiri ciki ba.

Haka nan yayin da yake ishara da makoma mai kyau na tattalin arzikin kasar Indiya da kuma irin albarkatun mai da iskar gas da Iran take da shi, wacce idan aka hada su biyun waje guda ana iya cewa Iran ita ce kasar da ta fi kowace hakan, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Baya ga mai da iskar gas, kamar yadda ka yi ishara, hanyar Chabahar daya ne daga cikin hanyoyi masu muhimmanci da suka hada gabashi da yammaci da kuma arewa da kudanci wadda za ta iya zama fagen da za a iya kulla alaka mai karfin gaske kuma mai amfani.

Har ila yau yayin da yake ishara da ingantacciyar siyasar gwamnatin Indiya na kin shiga cikin kowane guda da cikin hadin gwiwan kasashen yammaci da Amurka wai da sunan fada da ta'addanci, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Fada da ta'addanci na hakika yana iya zama daya daga cikin hanyoyin da Iran da Indiya za su iya aiki tare, don kuwa a fagen fada da ta'addanci wasu daga cikin kasashen yammaci ba da gaske suke yi ba. Saboda suna da hannu cikin kafa kungiyoyin ta'addanci a Afghanistan haka nan da kungiyoyin ta'addancin da suke kasashen Iraki da Siriya.

Haka nan yayin da yake jaddada cewar wajibi ne a mika batun fada da ta'addanci, wanda abin bakin ciki a yau ana yinsa ne da sunan Musulunci, ga musulmi da kasashen musulmi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Koda yake a fagen fada da ta'addancin kamata yayin lamurran su kasance a hannun kasashen musulmi wadanda ba ‘yan amshin shatan siyasar Amurka da kasashen yammaci ba ne, don kuwa wadancan kasashen ba su da niyyar fada da ta'addanci ta hakika.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Dangane da batun fada da ta'addanci, Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gaske take yi, sannan kuma za ta yi amfani da dukkan karfinta wajen fada da hakan.

Haka nan yayin da yake ishara da yadda kungiyoyin ‘yan ta'adda suke amfani da wasu daga cikin matsalolin da al'ummar musulmi take fuskanta a kasashensu wajen janyo hankulan matasa zuwa gare su da shigo da su cikin kungiyoyinsu, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: wajibi ne kasashen musulmin su yi kokari wajen kwace wannan makamin a hannun ‘yan ta'addan.

Jagoran ya bayyana ta'addanci a matsayin wata cuta mai yaduwa kana kuma mai hatsarin gaske yana mai cewa: Kamar yadda kowane ciwo mai tsanani yake da magani, to ta'addanci ma ana iya fada da shi sannan kuma a kawar da shi.

Shi ma a nasa bangaren, firayi ministan kasar Indiya Narendra Modi, wanda shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yake wa jagoranci, yayi ishara da ziyarar da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kai kasar Indiya a shekarar 1359 (1980) wanda ya ce ta kasance wata share fage wajen karfafa alaka tsakanin kasashen biyu. Daga nan sai ya ce: a yayin wannan ziyarar ma mun cimma yarjejeniyoyi masu kyau, wanda na yi imani cewa za a cimma sakamako mai kyau matukar bangarori biyu suka ba da himma.

Haka nan kuma yayin da ya ke jaddada maganar da Jagoran yayi dangane da hatsarin ta'addanci da kuma wajibcin fada da shi da dukkan karfi, Mr. Modi ya bayyana cewar: Abin bakin cikin shi ne cewa wasu kasashen sun rarraba ta'addanci zuwa ga "mai kyau" da "mara kyau", sannan kuma dangane da batun fada da ta'addanci maganar fatar baki kawai su ke yi.

Har ila yau yayin da yake jaddada cewa addinin Musulunci addini ne na soyayya da kauna sannan kuma ba shi da wata alaka da ta'addanci, firayi ministan kasar Indiyan ya bayyana cewar: A shekarun baya kasar Iran ta ba da shawarar gudanar da wani taron kasa da kasa don fada da ta'addanci amma wasu kasashen yammaci suka nuna adawarsu ga hakan.

Mr. Modi ya ci gaba da cewa: Wajibi ne kasashen da da gaske suke son fada da ta'addanci su hada hannuwansu waje guda da aiki tare wajen ganin bayan wannan annobar.

3500511

captcha