
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jawharafm.net cewa, Muhammad Khalil ya bayyana cewa sun raba kur’anai masu tarin yawa a dukkanin masallatan kasar, kuma suna ci gaba.
Ya kara da cewa dukkanin kur’anan dai an buga su ne bisa kira’ar Warsh daga Nafe da kuma Qalun daga Nafe, kuma ana sa ran za a kamala raba su nan yan kwanaki masu zuwa kafin fara azumi.
A bangare guda kuma ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Tunsia ta bayar da izini da a rika koyar da karatun kur’ani mai tsarki a makarantun gwamnati a ranakn hutu, domin amfanin dalibai.
Babbar manufar wannan shiri dai it ace wayar da kan dalibai dangane da hakikanin koyarwar addini, da kuma raba su da duk wata akida da za ta kai su ga shiga ayyukan ta’addanci da sunan addini.
Bisa ga wannan shiri dai yanzu haka ma’aikatar ilimi ta aince da hakan, kuma dalibai masu bukata za su iya zuwa a dukkanin ranakun hutu domin daukar karatun addini.