
Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alalam cewa, a yau kotun masarautar mulkin mulukiya ta iyalan gidan Saud ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 14 dukkaninsu masu fafutuka, saboda dalilai na siyasa.
An kame mutanen ne sakamakon gudanar da zanga-zangar da suka yi a yankunan gabashin Saudiyya tun 2011, domin nuna rashin amincewa da haramta musu hakkokinsu da ake yi a kasar, wadanda yankuna na gabashin Saudiyya dai yankuna ne na mabiya mazhabar shi'a na kasar.
Rahoton ya ce kotun ta jingina ayyukan ta'addanci a kan wadannan mutane, duk kuwa da cewa kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bayyana hukuncin da cewa na siyasa ne da bangaranci na banbancin mazhaba.
Al'ummar lardunan gabashin kasar Saudiyya wadanda mabiya mazhabar shi'a ne, suna kokawa dangane da yadda aka mayar da su saniyar ware a cikin dukkanin harkokin kasar tare da haramta musu hakkokinsu na 'yan kasa, duk kuwa da cewa daga yankunansu ne kasar take fitar da dukkanin man fetur da iskar gas wanda a kansa ne tatatlin arzikinta ya dogara.