Ya ce babu wani dalili da zai sanya masarautar Bahrain ta rike wannan babban mutum dan siyasa mai goyon bayan jama'ar kasa a cikin gidan kaso saboda mahangarsa ta siyasa.
A nasa bangaren kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bukaci mahukuntan kasar ta Bahrain da su sake tunani dangane da wannan danyen hukunci da suka yanke a kan wannan mutum mai fafutukar tabbatar da dimukradiyyar ta hanyar ruwan sanyi da zaman lafiya.
Tu a cikin watan Disanban shekara ta 2014 ne dai mahukuntan masarautar mulkin mulukiya ta kasar Baharain ta kame Sheikh Ali Salman, bisa a bin da suka kira barazanar da yake yi ga tsaro, saboda a cewarsu maganganunsa suna tunzura jama'a wajen kin tsarin wannan masarauta.
A cikin shekarun 1990 wannan masarautar ta kore shi daga kasar, amma ya dawo a cikin shekara ta 2001, sai dai a cikin shekara ta 2011 mutanen kasar sun mike suna neman a samu canjia cikin salon mulkin mulkiya da kasar take tafiya a kansa, inda ya taka gagarumar rawa wajen fadakar da al'umma kan hakkokinsu na yan kasa, inda ya kirayi masauratar da ta bayar da dama ga al'umma su gudanar da zaben yan majalisa wadanda za su rika wakiltarsu, maimakon ya zama sarki ne zai kafa majalisa kuma ya ayyana 'yan majalisa da yake so.
Wannan sayna masarautar ta sake dora karan tsana a kansa a cikin wadannan shekaru 5 da al'ummar suka mike suna nena canji daga mulkin kama karya da mulukiya.