IQNA

Jagoran Juyin Islama:

Riko Da Manufofin Juyi Shi Ne Hanyar Ci Gaba Da Kaiwa Ga Manufa

16:23 - June 04, 2016
Lambar Labari: 3480476
Bangaren siyasa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban dubban daruruwan mutane a hubbaren Imam Khomenei (RA) jagoran juyin islama Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, riko da manufofin juyin islama shi ne hanyar ci gaba da kuma cimma manufa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar Juma'a ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci gagarumin taron tunawa da shekaru 27 ga rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a), wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da aka gudanar a hubbaren marigayi Imam Khumainin da ke wajen birnin Tehran.

A jawabin da ya gabatar a wajen wannan gagarumin taro da ya hada da dukkanin bangarori na al'ummar Iran da baki ‘yan kasashen waje da jami'an diplomasiyyar kasashen duniya da suke Iran, Jagoran ya bayyana marigayi Imam Khumaini (r.a) a matsayin "mutum mumini mai yawan ibada kana kuma ma'abocin juyin juya hali", haka nan kuma yayin da yake jaddada wajibcin ci gaba da riko da "tafarkin juyin juya halin" a matsayin hanya guda daya tilo ta samar da ci gaba da tabbatar da manufofin al'umma da kuma tsarin Musulunci, Jagoran yayi Karin haske kan wasu siffofi masu muhimmanci guda biyar na riko da juyin juya halin yana mai cewa: Wajibi ne a yi amfani da kwarewar da aka samu yayin tattaunawar nukiliya, wato rashin ingancin aminta da Amurka, wajen ci gaba da tafiya bisa tafarkin ci gaban kasa.

Ayatullah Khamenei ya bayyana jumlar "mutum mumini mai yawan ibada kana kuma ma'aboci juyin juya hali" a matsayin wata cikakkiyar siffa ta marigayi Imam Khumaini (r.a) yana mai cewa: Maigirma marigayi Imam mutum ne mai "imani da Allah", "wanda yayi imani da matsayin mutane", "wanda yayi imani da manufar da aka sa gaba" sannan kuma "wanda yayi imani da tafarkin da zai kai shi zuwa ga wannan manufar".

Yayin da yake karin haske dagngane da siffar yawan ibadar marigayi Imam Khumaini (r.a), Jagoran ya bayyana cewar: Ya kasance salihin bawan Allah kana kuma ma'abocin kankan da kai ga Allah da kuma yawan addu'a.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da siffa ta uku da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya kebanta da ita, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Imam, ya kasance ma'abocin juyin juya hali, wanda wannan siffar ita ce ummul aba'isin din irin kiyayyar da masu tinkaho da karfi na duniya suke yi da shi.

Har ila yau yayin da yake bayanin cewa masu tinkaho da karfi na duniya suna tsananin adawa da riko da tafarkin juyin juya hali da al'ummar Iran suka yi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Babban dalilin irin matsin lamba kala-kala da ake wa al'ummar Iran tsawon shekaru ta hanyar fakewa da wasu dalilai na boge irin su batun nukiliya da take hakkokin bil'adamam shi ne saboda wannan siffa ta riko da juyin juya hali da al'ummar Iran da kuma gwamnatin Musulunci ta kasar suka yi ne.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da yadda kasar Iran ta kubuce daga hannun masu tinkaho da karfi na duniya da kuma yadda tsarin Musulunci na Iran ya zamanto wani abin koyi da kuma karfafa gwiwa ga sauran al'ummomin duniya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Hakikanin lamarin shi ne cewa Imam ma'abocin juyi ya ‘yanto kasar nan daga da dama daga cikin bala'oin da take ciki da suka hada "bala'oin dogaro (da manyan kasashen duniya), lalacewa ta siyasa, lalacewa ta halaye, kaskanci na kasa da kasa, koma baya na ilimi, tattalin arziki da fasaha da daukar Amurka da Ingila a matsayin sarakuna", sannan kuma ya haifar da gagarumin sauyi a tafarkin gudanar da kasar nan.

Har ila yau kuma yayin da yake fadin cewa marigayi Imam Khumaini (r.a) ya sauya tafarkin tafiyar kasar Iran zuwa ga tafarkin cimma manyan manufofin da aka sa a gaba, wato "tabbatar da ikon a addini, Ayatullah Khamenei ya ce: Kafa iko na addini yana nufin "tabbatar da adalci na zamantakewa na hakika", "tumbuke tushen talauci da jahilci", "tumbuke tushen rauni da cututtuka na zamantakewa", "tabbatar da koyarwar Musulunci", "tabbatar da lafiya ta jiki, kyawawan halaye da kuma ruhi", "tabbatar da ci gaban ilimi na kasa", "tabbatar da daukaka, mutumci na kasa da kuma karfi na kasa da kasa" da kuma "karfafa irin dama da albarkatun da ake da su a cikin kasa".

Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar albarkacin juyin juya halin Musulunci, marigayi Imam Khumaini (r.a) ya samu damar juya kasar Iran zuwa ga tafarkin cimma wadannan manufofin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Duk kuwa da cewa kai wa ga wadannan manufofin, wani lamari ne da ke bukatar lokaci da kuma kokari, to amma duk da haka dai za a iya cimma su. Kawai dai sharadin cimma su din shi ne tafiya bisa tafarkin juyin juya hali da kuma riko da wannan tafarkin.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Bayan rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a), a duk lokacin da muka yi aiki da ruhi irin na juyin juya hali, to kuwa mun sami ci gaba. Sannan kuma a duk lokacin da muka nuna gazawa da kuma gafala da riko da tafarkin juyin juya hali da tafarkin jihadi, to kuwa mun ci baya da kuma fuskanta rashin nasara.

Don haka sai ya kirayi dukkanin bangarori na al'ummar Iran da cewa: Lalle za a iya tafiya a bisa wannan tafarkin ta hanyoyi da salo mabambanta, wanda idan aka sami hakan to ko shakka babu za a sami ci gaba, kamar yadda kuma za a iya yin hakan ta wata hanyar ta daban wanda a irin wannan yanayin kan lalle makomar kasar, al'ummar Iran da kuma shi kansa addinin Musulunci za su fuskanci koma baya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana juyin juya halin Musulunci a matsayin wani gagarumin jari maras tamka ga al'ummar Iran da kuma kasar baki daya yana mai cewa: Kafin kai wa ga nasarar da juyin juya halin Musulunci ya samu, lalle an yi gagarumar sadaukarwa, to sai dai kuma tare da wadannan sadaukarwar an cimma wasu abubuwa masu yawan gaske.

Yayin da yake ishara da irin karfin da juyin juya halin Musulunci yake da shi bayan shekaru 37 da nasararsa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A halin yanzu dai yanayin al'ummar Iran ya fi na shekarun baya kyau.

Jagoran ya jaddada cewar: juyin juya halin Musulunci yayi nasara ne albarkacin azama, irada da kuma imanin mutane, sannan kuma saboda irin wannan karfi na mutane ne ya ci gaba da wanzuwa da kuma tsayin daka wajen tinkarar barazana ta soji da takunkumin, ya ci gaba da tsayuwa da kafarsa da kuma ci gaba da bin tafarkinsa cikin jaruntaka da daukaka, wanda a nan gaba ma wajibi ne a ci gaba da riko da wannan tafarkin.

Yayin da yake magana kan cewa riko da juyin juya hali ba wai kawai lamari ne da ya takaita ga lokacin gwagwarmaya da kuma zamanin marigayi Imam Khumaini (r.a) ba, Ayatullah Khamenei ya ce: Juyin juya hali da kuma riko da koyarwar juyin na dukkanin zamunna ne. juyin juya hali wani lamari ne mai ci gaba da tafiya, don haka dukkanin wadanda suka yi riko da wadannan siffofi na juyin juya hali, ma'abota juyin ne, hatta matasan da ba su ga marigayi Imam Khumaini (r.a) ba.

Haka nan kuma yayin da ya ke bayyana kuskuren mahangar wasu mutane da suke daidaita riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci da tsaurin ra'ayi da wuce gona da iri da kuma raba al'ummar Iran zuwa gida biyu, wato "masu ra'ayin rikau" da "masu sassaucin ra'ayi", Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Lalle bai kamata a bari wannan fassara ta ‘yan kasashen waje da kuma makiya ta shigo cikin fagen siyasar kasar nan ba.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da wani kuskuren da ake yi dangane da batun juyin juya halin Musulunci da riko da tafarkinsa, Jagoran ya ce: Fatan ganin salo irin daya na riko da tafarkin juyin juya halin Musulunci a gurin dukkanin mutane da suke tafiya a bisa tafarki da mahangar juyin juya halin Musuluncin, shi ma kuskure ne. Abin da ke da muhimmanci shi ne samar da siffar riko da koyarwar juyin juya halin Musuluncin.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne a samu tafiyar wani a bisa tafarkin juyin juya halin Musulunci ta zamanto ta fi kyau, mai yiyuwa kuma wani bai rike hakan da kyau ba, to amma dukkaninsu ma'abota juyin juya halin ne. Babu yadda za a tuhumci wani mutum wanda yake bisa tafarkin juyin juya halin sai dai bai yi tafiyarsa da kyau ba da rashin riko da juyi ko kuma gaba da juyin ba.

Yayin da ya ke karin haske dangane da siffofi na asali na riko da juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Khamenei yayi ishara da wasu siffofi guda biyar na asalin wadanda su ne: "Riko da tushe da koyarwa na asali na juyin juya halin Musulunci", "Kokari wajen cimma manufofi da koyarwar juyin da kuma aiki tukuru wajen cimma su", "Riko da cikakken ‘yancin kan kasa", "Nuna damuwa ainun a kan makiya da kuma rashin mika musu wuya" da kuma "tsoron Allah na addini da na siyasa".

Yayin da yake karin haske dangane da siffa ta farko ta riko da juyin juya halin Musuluncin, wato "Riko da tushe da kuma koyarwa na asali na juyin juya halin Musulunci", Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: "Riko da kuma imani da Musulunci na hakika a gaban Musulunci samfurin Amurka" shi ne babban tushen wannan siffa (ta farko).

Jagoran ya ci gaba da cewa: Musulunci samfurin Amurka yana da rassa biyu, wadanda su ne "Musulunci da aka bar shi a baya" da "Musulunci da babu ruwansa da addini", wanda ma'abota girman kan duniya suna goyon bayan dukkanin wadannan rassa biyun.

Ayatullah Khamenei ya bayyana "imani da irin matsayin da mutane suke da shi" a matsayin wani bangare na koyarwar juyin juya halin Musulunci inda ya ce: A tsarin Musulunci, ra'ayi, bukatu da manufofin mutane su ne tushe. A saboda haka imani a kuma riko na hakika ga wannan lamari, suna daga cikin wajibai na riko da juyin juya halin Musulunci.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana "ci gba da kuma samun kamala" a matsayin wasu siffofi na daban na riko da koyarwar juyin juya halin Musuluncin inda ya ce: Wajibi ne mutum mai riko da juyin juya hali ya zamanto yayi imani da wannan siffa da kuma c igaba da kyautata ta.

"Goyon bayan raunana da marasa shi" da kuma "goyon bayan wadanda ake zalunta a duniya" wasu siffofi na riko da koyarwar juyin ne da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi bayani kansu a matsayin wani bangare na siffa ta farko ta riko da koyarwar juyin da yayi ishara da ita a baya.

Jagoran ya ci gaba da cewa:Idan har aka yi riko da hakan ko kuma kamar yadda Alkur'ani mai girma ya bayyana aka samu tsayin daka, to kuwa tafiya da ayyukan jami'an gwamnati da kuma shi kansa tsarin Musulunci zai samu tsayin daka da kuma tsayuwa kyam a gaban dukkanin matsaloli. Idan kuwa ba haka ba, matukar muka fuskanci matsalar rashin tabuka komai, to komai kashin matsala, za ta sauya mu daga tafarkin da muke kai.

Daga nan kuma sai Ayatullah Khamenei ya koma kan bayanin siffa ta biyu ta riko da juyin juya halin Musuluncin, wato "kokari ba kama hannun yaro wajen samun ci gaba da kuma isa ga manufofin juyi" inda ya ce: Bai kamata komai rintsi ko tsanani mu yi kasa a gwiwa wajen kokarin isa ga manyan manufofin juyin juya hali da kuma al'umma ba, ko kuma mu ji mun wadata da irin yanayin da muke ciki a halin yanzu ba.

Jagoran ya bayyana "ragwantaka da rashin kyakkyawan fata" a matsayin kishiyar wannan siffa yana mai cewa: Hanyar ci gaba dai ba ta karewa, wajibi ne a ci gaba da bin wannan tafarki ta hanyar riko da tafarkin juyi.

Siffa ta uku ta riko da tafarkin juyin da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da ita cikin jawabin nasa a wajen bikin juyayin shekaru 27 da rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) ita ce "riko da ‘yancin kai na kasa" wanda yayi karin haske kanta cikin bangarorinta guda uku na siyasa, al'adu da kuma tattalin arziki.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Ma'anar ‘yanci na siyasa na hakika ita ce kada mu fada tarkon yaudara ta makiyi, sannan kuma a dukkanin yanayi mu yi kokarin wajen tabbatar da ‘yancin kai na cikin gida, yanki da kuma duniya.

Yayin da yake ishara da salon yaudara na makiya musamman Amurka, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wadannan mutane ba wai suna amfani da barazana a koda yaushe ba ne, a wasu lokuta hatta da fara'a da ma wasu maganganu masu janyo hankali suke amfani. Ga misali su kan rubuta wasika suna cewa ku zo mu tattauna da hada kai waje guda don magance matsalolin duniya. A irin wannan yanayi mai yiyuwa ne mutum ya fada tarkon waswasi da jin cewa abu ne mai kyau mu tafi mu zauna da wata babbar kasa ta duniya don magance matsalolin duniya. Alhali ya gafala da cewa a badini wannan makiyin yana son cimma wata manufa ce ta daban.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Abin nufi da kiran da makiyi yayi wajen aiki tare don magance matsalolin duniya, shi ne neman taimako da taka rawa wajen magance matsalolin duniya a fagen da ya tsara.

Yayin da yake kafa misalin haka, Jagoran yayi ishara da abin da ke faruwa a kasar Siriya inda ya ce: Dalilin da ya sanya muka ki shiga abin da ake kira hadin gwiwan Amurka wajen fada da ta'addanci a Siriya da sauran wajaje makamancin wannan, shi ne cewa mun riga da mun san cewa suna son amfani da irin matsayi da tasirin da muke da shi da kuma na sauran kasashe wajen cimma manufofinsu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Irin wadannan ayyukan wadanda a zahirinsu ba su saba wa ‘yancin kai ba, amma a aikace suna nufin taimakawa makiya cikin ayyukansu ne, wanda kuma a hakikanin gaskiya yayi hannun riga da ‘yancin kan kasa.

Yayin da yake karin haske dangane da reshe na biyu na siffar ‘yancin kan, Ayatullah Khamenei ya jaddada muhimmancin ‘yanci na al'adu yana mai cewa: Riko da koyarwar juyin juya hali yana nufin "zaban irin salon rayuwa na Musulunci da Iran" da kuma "nesantar koyi da al'adun kasashen yammaci da ‘yan kasashen waje".

A saboda haka ne Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da irin hanyoyin sadarwa na zamani irin su internet a matsayin kayan aikin da kasashen yammaci suke amfani da su wajen tattaro bayanai da yada al'adunsu a tsakanin al'ummomin duniya yana mai cewa: Wadannan hanyoyi, duk kuwa da cewa ana iya amfani da su ta hanyoyi masu amfani, to amma wajibi ne a yi kokarin kange ikon makiya a kansu, a yi aiki ta yadda wadannan hanyoyin sadarwar ba za su zamanto wata hanyar ta tabbatar da tasiri da ikon makiya akan al'adunmu ba.

Batu na gaba da Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi karin haske kansa a yayin da yake bayanin siffa ta uku ta riko da juyin juya halin Musulunci, wato tabbatar da ‘yancin kai na gaba daya na kasa, shi ne cewa " ‘yancin kai na tattalin arziki" ba yana nufin rashin shiga cikin tattalin arziki na duniya da kasa da kasa ba ne.

Jagoran ya bayyana cewar: Bayan yarjejeniyar nukiliya, Amurkawa sun bayyana cewar: Wajibi ne yarjejeniyar nukiliya da Irana ta zamanto hanyar shigar da tattalin arzikin Iran cikin na duniya. Ma'anar wannan maganar ita ce cewa a shigo da Iran cikin taswira da kuma tsarin da ‘yan jari hujja wadanda mafiya yawansu sahyoniyawa ne suka tsara don tabbatar da manufofinsu na tattalin arziki.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Amurkawa sun sanya wa Iran takunkumi ne don raunana tattalin arzikin Iran. A halin yanzu ma da aka cimma yarjejeniyar, suna son shigo da tattalin arzikin Iran da dulmuya shi cikin tsarin tattalin arziki na duniya da ‘yan jari hujjan Amurka suka tsara.

Ayatullah Khamenei ya bayyana tattalin arzikin dogaro da kai a matsayin hanya guda kawai ta tabbatar da ‘yancin kai na tattalin arziki a Iran yana mai cewa: Abin farin cikin shi ne cewa bisa rahotannin da aka bayar, gwamnati ta fara wasu ayyuka a wannan shekarar ta tabbatar da tattalin arziki na dogaro da kai, wanda matukar aka ci gaba da hakan, ko shakka babu mutane za su ga tasirinsa.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne a dukkanin ayyukan da gwamnati za ta yi cikin kuwa har da yarjejeniyoyin da za a kulla ya zamana an kula da tattalin arziki na dogaro da kai da kuma ba shi muhimmanci.

Daga nan sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi karin haske kan siffa ta uku ta riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci, wato "Nuna damuwa da yin taka tsantsan kan ayyukan makiya".

Jagoran ya bayyana cewar: Tamkar fagen daga, wajibi ne a dinga sanya ido kan duk wani yunkuri na makiya da kuma yin sharhi kansu. Wajibi ne a fahimci manufarsu, sannan kuma a zama cikin shirin tinkarar duk wani aiki na su na kiyayya.

Haka nan kuma yayin da yake kakkausar suka ga mutanen da suke rufe ido kan irin kiyayyar da Amurka take nuna wa al'ummar Iran a fili, Ayatullah Khamenei ya ce: Inkarin kiyayyar da Amurka take nuna wa Jamhuriyar Musulunci da kuma al'ummar Iran a fili, wani makirci ne na rage irin damuwa da kyamar babbar Shaidaniyya (Amurka).

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kiyayyar da Amurka take yi da juyin juya halin Musulunci da cewa wata kiyayya ce dake cikin zatinta yana mai cewa: Gwamnatocin ‘yan mulkin mallaka suna tabbatar wa da duniya hakikaninsu ta hanyar dabi'arsu ta neman fada, goyon bayan ta'addanci, dirar mikiya a kan masu neman ‘yanci da kuma zaluncin da suke yi wa al'ummar Palastinu da ake zalunta. A saboda haka gwamnatin Musulunci ba za ta iya zama ‘yar ba ruwanmu a gaban wannan zaluncin ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana taimako kai tsaye da Amurka take ba wa kasar da take kai hare-hare kan al'ummar Yemen a matsayin tarayya cikin kashe mutanen da ba su ci ba su sha ba. Daga nan sai ya ce: Bisa koyarwar Musulunci, ba za a iya yin shiru kan wannan danyen aikin ba.

A yayin da yake rufe wannan bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya ce: Duk wani mutum ko wata kungiyar da take aiki don Musulunci kuma da sunan Musulunci, matukar ta yarda da Amurka, lalle ta yi babban kuskure kuma za ta fada tarkonta.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Cikin shekarun baya-bayan nan wasu daga cikin kungiyoyin Musulunci a yankin nan da suna dabara ta siyasa da hikima, sun fara hada kai da Amurkawa. To amma a halin yanzu sun fada tarkon Babbar Shaidaniyya.

Ayatullah Khamenei ya bayyana Ingila a matsayin wata abokiyar gabar al'ummar Iran ta hakika yana mai cewa: Babu wani lokaci da turawan Ingila suka taba barin kiyayyarsu a kan al'ummar Iran.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A ci gaba da irin wannan kiyayyar ta su ne ya sanya cibiyar farfaganda da labaran Ingila a wadannan ranaku na tunawa da rasuwar marigayi Imam, da taimakon Amurka, ta tsara wasu bayanai marasa inganci dangane da tarihin rayuwar Imam da nufin bata sunansa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana haramtacciyar kasar Sahyoniyawa a matsayin wata abokiyar gabar al'ummar Iran tamkar yadda Amurka da Ingila suke. Daga nan sai ya ce: Wajibi ne sanya ido sosai kan ayyukan makiya sannan kuma a yi taka tsantsan dangane da duk wata shawara da za su baya ciki kuwa har da a bangaren siyasa da tattalin arziki. Idan har aka sami irin wannan yanayi, to batun rashin mika musu wuya ma zai shigo fage, wanda hakan shi ne wannan "Jihadi mai girma" da ake magana kansa.

Har ila yau kuma yayin da yake bayanin siffa ta karshe na riko da juyin juya hali, wato "tsoron Allah na addini da siyasa", Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Tsoron Allah na addini shi ne dai wannan kokari da sanya ido wajen cimma manufofin da koyarwar Musulunci wajen ciyar da al'umma gaba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A wannan fagen bai kamata a dogara kawai da lissafi na hankali ba, don kuwa kokarin cimma wadannan manufofin, wani takalifi ne na addini. Duk wanda ya raba bangaren siyasa na musulunci da bangarensa na zamantakewa, to lalle bai fahimci Musulunci ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Matukar aka samu tsoron Allah na addini, to kuwa za a sami tsoron Allah na siyasa. Hakan kuwa zai kare mutum daga zamewa ta siyasa da kuma sauke nauyi na jagoranci da ke wuyansa.

Bangaren karshen na jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin a wannan taro na tunawa da rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) ya kebanta da bayanin wasu shawarwari da kira masu muhimmancin gaske wanda na farkonsu shi ne "Kallon Imam a matsayin wani cikakken abin koyi".

Dangane da hakan, Ayatullah Khamenei ya ce: A taswirar hanyar da a yau muka yi bayaninta, Imam ya kasance ya mallaki dukkanin wadannan siffofi a yanayi na koli. A saboda haka wajibi ne a dauke shi a matsayin wani cikakken abin koyi da kuma ba wa hakan muhimmanci.

Jagoran ya bayyana dubi da kuma tuntuni cikin maganganun marigayi Imam Khumani da wasiyyarsa da kuma debe kewa da riko da maganganu da mahangarsa a matsayin wata hanya ta riko da shi a matsayin abin koyi. A saboda haka ya kirayi dukkanin al'umma musamman matasa da su yi riko da wannan lamari.

Kira da kuma shawara ta biyu da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar ita ce "rashin mancewa da irin kwarewar da aka samu a yayin tattaunawar nukiliya.

Jagoran ya ce: Wannan kwarewar tana koyarwar da mu cewa a yayin tinkarar Amurka ko da kuwa mun yi sassauci da saukowa, to ita kuwa ba za ta taba barin makircin da take yi mana ba.

Yayin da yake ishara da tattaunawar Iran da kasashen 5+1 da kuma tattaunawa ta bangarori biyu tsakanin Iran da Amurka dangane da batun nukiliya, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Sakamakon kokarin ‘yan'uwanmu, an cimma yarjejeniya, to amma har ya zuwa yanzu Amurka tana ci gaba da karya alkawari da kin sauke nauyin da ke wuyanta.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Kafin wannan tattaunawa ta nukiliya da dama suna da masaniya kan irin wannan dabi'a ta Amurka kuma ma suna fadin hakan, to amma wasu ba su sani ba, wanda a halin yanzu ya kamata su sani.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Idan har a dauka ne, wanda kuma hakan ma ba zai yiyu ba, idan har a dauka a dukkanin fagage cikin su kuwa har da batun hakkokin bil'adama, makamai masu linzami, ta'addanci, Labanon, Palastinu da sauran batutuwa, za mu zauna teburin tattaunawa da Amurka, sannan kuma mu yi kasa a gwiwa da kuma saukowa kasa daga matsayarmu, to lalle ita Amurka ba za ta taba saukowa. Bayan sakin fuska da dariya da maganganu na fatar baki, a bangare guda manufarsu za su ci gaba da ganin sun cimma.

Shawara ta uku da Imam ya bayar ita ce "tabbatar da hadin kai tsakanin gwamnati da al'umma".

Jagoran ya bayyana cewar: Mai yiyuwa ne wani ya yarda da gwamnatin da take mulki wani kuma bai yarda da ita ba, hakan babu laifi cikinsa, amma wajibi ne a kiyaye hadin kan da ke tsakanin gwamnati da al'umma.

Jagoran ya ce babu laifi a soki gwamnati kan wasu ayyuka da siyasarta, hakan bai saba wa hadin kai ba, to amma wajibi ne a yi taka tsantsan kada a haifar da kiyayya da gaba.

Shawara ta hudu da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar ita ce dangane da "sansani masu kokarin ganin bayan tsayin daka da fadar da bakar siyasar Amurka".

Jagoran ya bayyana cewar: Amurka ita ce kan gaba a wannan fagen, amma rassan hakan sun yadu zuwa wasu wajaje a wasu lokuta ma har cikin kasar nan sun iso. A saboda haka wajibi ne a yi taka tsantsan da boyayyun rassa da ayyukan wannan kungiya.

"Shata kan iyaka da makiya" ita ce shawara da kira ta biyar da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi a yayin jawabin nasa wajen bikin tunawa da shekaru 27 da rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a).

Jagoran ya bayyana cewar: Wasu daga cikin kungiyoyi a cikin gida, sakamakon gafala da wannan lamarin, sun gaza wajen kiyaye kan iyakokin da aka shata, haka nan kuma kan iyakoki ma da aka shata sun yi rauni da kuma fara gogewa. Don haka wajibi ne mu yi taka tsantsan wajen ganin kan iyakokin da aka shata tsakaninmu da makiyan juyin juya halin Musulunci da Imam da al'ummar Iran bai goge ba.

Shawara ta karshe da Ayatullah Khamenei ya bayar ga al'umma da kuma jami'an gwamnatin Iran ita ce: Yarda da kuma dogaro da gaskiyar alkawarin taimako na Ubangiji da kuma cewa lalle makoma mai kyau tana tare da al'ummar Iran da matasan Iran ko da kuwa makiya ba sa so.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci sai da Hujjatul Islam wal muslimin Sayyid Hasan Khumaini, jikan Imam kuma mai kula da haramin Imam Khumaini (r.a) ya gabatar da jawabinsa na maraba da mahalarta taron inda ya bayyana juyin juya halin Musulunci a matsayin wani juyi na Ubangiji kana kuma wanda ya sami goyon bayan al'umma. Sayyid Hasan ya ce juyin yayi nasara ne sakamakon taimako na Ubangiji da goyon bayan da al'umma suka ba wa marigayi Imam Khumaini (r.a) wanda ya kasance wani babban bawan Allah mai siffofi na musamman, sannan kuma bayan rasuwar Imam, juyin ya ci gaba da tafiya ne sakamakon zaban wani mutum wanda ya dace kwarai wajen ci gaba da wannan aiki na marigayi Imam Khumaini.

3503614

captcha