
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Associated Press cewa, Obama ya isar da sakon nasa kamar yadda yasaba a kowace shekara, tare da bayyana cewa wannan wata lokaci na ibada da tsarkake zuciya da kuma yin yafiya.
Oabam ya ce Amurka kasa ce wadda ta hada mabiya addinai daban-daban da suka hada da musulmi,kuma ana kare hakkokinsu kamar yadda ake kare hakkin kowane dan kasa, domin kuwa a cewarsa kasarsa kasa ce mai girmama hakkin dan adam.
Wannan furuci na Obama dai ya zo a daidai lokacin da dan takarar shugabancin kasar Amurka a karkashin inuwar jam’iyyar Republican Donald Trump yake ta kara bayyana matsayinsa nag aba ga addinin muslunci da kuma musulmi.
A cikin yan lokutannan dai sakamakon hare-haren ta’addancin da masu dauke da akidar kafirta musumlmi suke kaiwa a cikin kasashen yammacin turai, kyaar addinin muslunci ta karu matuka.
Gwamnatin Obama tana a sahun gaba wajen sayar da makamai ga kasashen larabawan yankin gabas ta tsakiya da suke yada akidar ta’addanci.