
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkafeel.net cewa, an kawo karshen bangare na farko na gasar kur’ani ta Karbala da aka gudanmar a cikin kwanaki shida.
Gasar wadda aka fara tun daga kusan mako guda da ya gabata, an gudanar da ita ne a bangaren farko tare da halartar rukuni 16 da ya kunshi makaranta da mahardata da kuma masu tafsiri.
Wannan gasa dai cibiyar horar da makaranta da mardata kur’ani ta hubbaren Abbas (AS) ce ta dauki nauyin shiryata akaro na shida, kuma an fara ne da rukuni 24 inda aka kamala bangaren farko na rukuni goma sha shida.
Za a shiga bangare na biyu na gasar da rukunoni gonma sha shida, haka nan kuma za a ci gaba har zuwa ga mataki na karshe, inda za a gudanar da gasar da za a fitar da wadanda suka nuna kwazo daga dukkanin bangarori na gasar.
Ana watsa wannan gasa kai tsaye a wasu kafofin yada labarai ma kasar, wadda kuma take samu halartar mutane daga larduna goma sha biyu na kasar, daga masu watsa wannan gasa akwai tashar talabijin ta Alfurat.