IQNA

Jagoran Juyin Isalam:

Amurka Na Ha'intar Mutane Kan Batun Yarjejeniyar Nukiliya

23:53 - June 21, 2016
Lambar Labari: 3480535
Bangaren siyasa, a lokacin da yake ganawa da masana da kuma mawaka daga sassa na kasar da kuma wasu kasashe makwafta, jagoran juyin juya halin ya bayyana Amurka a matsayin mai yaudarar jama'a da batun yarjejeniyar nukiliya.

Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yammacin Litinin wacce ta yi daidai da daren ranar haihuwar Imam Hasan al-Mujtaba (a.s), Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wasu gungun mawaka da masana adabin harshen farisanci na kasar Iran bugu da kari kan wasu mawakan da suka fito daga kasashen Pakistan, Indiya da Afghanistan.

A jawabin da ya gabatar yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana mawaka a matsayin wani jari mai kimar gaske na kasar Iran, sannan kuma yayin da yake jaddada wajibcin rayarwa da kuma tabbatar da ganin cewa wakokin da ake yi sun yi daidai da batutuwa da bukatun da ake bukatarsu a kasa, Jagoran ya bayyana cewar: A halin yanzu dai ana cikin halin yaki ne na kwakwalwa da fata ta siyasa da al'adu. A saboda haka wajibi ne a yi amfani da wakoki a matsayin wani makami mai tasiri a wannan fagen.

Haka nan kuma yayin da yake jinjinawa marigayi Hamid Sabziwari, (sanannen mawakin juyin juya halin Musulunci na Iran din nan da ya rasu kwanakin baya), Jagoran ya bayyana kwarewa wajen amfani da kalmomi da jumloli a matsayin wasu daga cikin siffofin da wannan mawakin ya kebanta da su. Daga nan kuma sai ya ce: Siffa maras tamka da Marigayi Sabziwari ya kebanta da ita ita ce yin wakoki masu tasirin gaske kana kuma wadanda suka dace sosai.

Daga nan sai Ayatullah Khamenei ya ci gaba da bayanin matsayi da kuma nauyin da ke wuyan waka, inda ya bayyana mawaka a matsayin daya daga cikin mafiya girma da daukakan jarin kasar Iran, yana mai cewa: Wajibi ne a shigo da waka cikin fagage irin na siyasa, al'adu, alaka da mutane da rayuwa ta zamantakewa da kuma fada da makiya na waje e a lokacin da kasar Iran take bukatar hakan, don biyan wannan bukata ta kasa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wajibi ne waka ta zamanto a raye, sannan kuma ta taka nata rawar cikin lamurran da ke gudana da kuma bukatuwa ta kasa.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana wajibcin yadawa da kuma kwadaitar da wakoki da rayar da su, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da irin nauyi da rawar da hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran da sauran cibiyoyin da ke gudanar da ayyukansu a wannan bangaren za su taka a wannan fagen inda ya ce: A halin yanzu sama da shekarun baya ana rera wakoki kan batutuwa irin su Palastinu, Yemen, Bahrain, Kallafaffen yaki, shahidai masu kare hubbarorin Imaman Ahlulbaiti (a.s) ko kuma zaluncin da aka yi wa mujahidai irin su Sheikh Zakzaky, wannan jarumi kana tsayayyen malami na Nijeriya da aka zalunta, to amma abin bakin cikin shi ne cewa ba a yadawa da kuma bayyanar da irin wadannan wakokin yadda ya dace. Lalle akwai gazawa a wannan bangaren.

Ayatullah ya bayyana "bayyanin irin ha'inci da rashin cika alkawarin Amurka cikin yarjejeniyar nukiliya da aka cimma" a matsayin daya daga cikin fagagen da za a iya rayar da wakoki da su, inda ya ce: Baya ga ‘yan siyasa, wajibi ne su ma masu ayyuka na al'adu musamman mawaka su yi wa mutane wannan lamarin.

Haka nan kuma yayin da yake kakkausar suka ga wasu matakan da ake dauka kan mawaka a wasu wajajen, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Abin bakin cikin shi ne cewa a wasu lokuta a kan girmama wasu mutane da ba su da komai kashin riko da girmama koyarwa Musulunci da kuma juyin juya halin Musulunci, to amma ba a kula da kuma jinjinawa mawakin da ya ba da dukkanin rayuwarsa da kwarewar da yake da ita a bisa tafarkin Musulunci da juyin juya halin Musulunci.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Duk da cewa fagen daga da yaki na yanzu ya bambanta da na farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, wanda a halin yanzu muna fagen yaki na tunani da kwakwalwa ne, yaki na siyasa, al'adu, tsaro da kuma fada da kokarin yin tasirin makiya, wato tunani da iradoji ne suke yaki da junansu. Don haka waka tana daga cikin makamai masu tasirin gaske a wannan yakin.

Don haka Jagoran ya kirayi mawakan zuwa ga kara karfafawa da kuma kyautata yanayin wakokin na su don cimma wadannan manufofi da aka shata.

Tun da fari dai sai da wasu mawaka 23 daga cikin mahalarta taron suka gabatar da wakokinsu.

A karshen ganawar dai, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jagoranci mahalarta taron sallolin Magariba da Lisha, kana kuma suka sha ruwa tare.

3508985

captcha