
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Jaridar Washington Post ta habarta cewa, Rev Christopher Rodkey ya saka wani allo ne a cikin harabar majami'arsa wanda a cikinsa ya rubuta fatan alkhairi ga musulmi dangane azumin watan ramadan, wanda hakan ya sanya wasu masu adawa da musulunci a cikin unguwar suka yi ca a kansa, daga cikinsu kuwa har da wani dan majalisar dokokin kasar Amurka a karkashin inuwar jam'iyyar Republican, wanda yake goyon bayan Donald Trump.
Rev Christopher Rodkey wanda malamin kirista ne kuma malami ajami'a a Pennsylvania, ya sheda wa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa, shi yana girmama dukkanin addinai, musamman ma addinin muslunci wanda addini ne da aka safkar daga sama, kuma akwai abubuwa da dama da suka hada musulmi da kirista na imani, saboda haka duk wanda ya soke shi kan taya musulmi murnar azumi to ganinsa jahili ne da bai san addinin kirista ba.