IQNA

Mahukuntan Bahrain Na Daukar Nauyin Jaridu Domin Cin Zarafin Wani Bangaren Al'umar Kasar

22:39 - July 03, 2016
Lambar Labari: 3480577
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Bharain na daukar nauyin wasu daga cikin jaridun kasar domin cin zarafin manyan jagororin bangaren masu rinjaye daga cikin al'ummar kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Manama Post wadda ta rubta a shafinta na yanar gizo cewa, masarautar mulkin mulukiya ta Al Khalifa akasar Bahrain tana sayen wasu daga cikin 'yan jaridar kasar da take da alaka da su, domin bata sunan wasu fiattun mutane da al'ummar kasar ke ganin kimarsu, sakamakon mahangarsu ta siyasa, ko kuma banbancin fahimta ta mazhaba.


Bisa ga rahoton wannan jarida masautar ta Bahrain ta ware makudan kudade domin gudanar da wannan aiki, dukkanin mutanen da ake nufin bata sunansu ta wannan hanyar kuwa manyan malaman addini ne na mabiya mazhabar shi'a a kasar, sai kuma fitattun 'yan siyasa da kuma shugabannin cibiyoyin farar hula da na kare hakkin bil adama a kasar, matukar dai mabiya mazhabar shi'a ne.

Mahukuntan Bahrain wadanda 'yan sunna ne da turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mika wa ragamar mulkin kasar kafin ficewarsu, sun jima suna daukar matakan gallazawa ga mabiya mazhabar shi'a a kasar wadanda su ne fiye da kashi 85 cikin dari na al'ummar kasar, inda lamarin ya kara tsananta a baya-bayan nan, sakamakon kran da suke na a yi adalci a cikin sha'anin mulki da siyasa, ta hanyar kafa majalisar dokoki wadda al'umma za su zaba da kansu, maimakon yadda ake yi yanzu, inda sarki ne da kansa ke nada 'yan majalisa, kuma su aiwatar da abin da ya ga dama a cikin majalisar.

Wasu daga cikin kafofin yada labarai na sarakunan mulkin kama karya daga cikin kasashen larabawan yankin tekun fasha, da suka hada da na Qatar, Saudiyya da kuma hadaddiyar daular larabawa, suna yin aiki tukuru wajen yada wanann manufa ta masarautar Bahrain.

Matkin baya-bayan nan da masarautar mulkin kama karya ta Bahrain ta dauka shi ne rusa jam'iyyar Alwifaq, jam'iyyar siyasa mafi girma a cikin dukkanin kasashen larabawan yankin tekun fasha, tare da janye izinin zama dan kasa daga kan Ayatollah Sheikh Isa Kasim babban malamin addi mafi karfin fada aji a kasar.

3512042

captcha