IQNA

An Kawo Karshen Gasar Kur’ani ta Radio A Mauritania

22:15 - July 04, 2016
Lambar Labari: 3480580
Bangaren kasa da kasam an kawo karshen gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta radio a Mauritania.

Kamfanin dillancin labaran Kur’ani na Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aqlame.com cewa, gidan radiyon gwamnatin kasar Mauritaniya ne ya dauki nauyin wannan gasa.

An kamala wannan gasa ne a babban masalacin Ibn Abbas da ke birnin Nuwakshout fadar mulkin kasar, wadda Sayyid Wuld Abdulaziz shugaban kasar ya dauki nauyinta, tare da halartar wasu daga cikin jami’an gwamnatin kasar.

Sayyid Abdullah Wuld Yakub Wuld Hurmatullah ya ce tun daga ranar da aka fara gudanar da gasar an ta watsa kai tsaye a gidan radiyon kasar Mauritania, lamarin da ya kara armashin gasar, inda mutane suke saurare kai tsaye daga gidajensu a fadin kasar.

An gudanar da gasar a matakin share fagea cikin watan Sha’aban ne, inda mutane 140 suka samu nasarar tsallakewa zuwa ga mataki na karshe, wadanda su ne suka kara da juna har zuwa karshen gasar a yau.

Za afitar da sakamakon gasar ne bayan kwamitin da aka kafa ya mamala aikinsa na tantancewa, daga nan kuma za a mika sakamakon ga Allamah Muhammad Mukhtar Wuld Ambalah babban mai bayar da fatawa na kasar.

  1. 3512369

captcha