
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga Jaridar Daily Beast ta bayar da rahoto a shafinta na yanar gizo cewa, wasu mutane uku ne dauke da makamai suka yi ruwan harsasai a kan likitan a lokacin da yake tafiya zuwa masallaci, jim kadan bayan harbinsa sun tsere bisa zaton cewa ya rasu, amma nan da nan an kawo masa dauki inda yanzu haka ake kula da shia wani asibiti da ke cikin jahar ta Texas, duk kuwa da cewa har yanzu yana cikin mawuyacin hali.
Jami'an 'yan sanda suna ta kokarin nisanta abin da ya faru da kyamar da ake nuna ma muuslmia cikin wanann jaha, inda suke danganta lamarin da wani abu na daban, amma musulmin da suke yi salla tare da shi sun bayyana cewa hakika su kansu sau tari suna fuskantar barazana daga mutane masu kyamar musulunci.
Wannan dai shi ne karo na uku da aka kaiwa musulmi hari a cikin kasar Amura a wanann mako da muke ciki, inda ko a ranar Asabar da ta gabata, wasu masu kyamar addinin muslunci sun kai hari kan wani musulmi a cikin jahar Florida, inda shi ma suka jikkata shi, kamar yadda a jiya Litinin ma wasu sun kai farmaki kan wasu matasa biyu muuslmi a babban birnin kasar.