IQNA

Musulmin Birtaniya Sun Damu Kan Thereza Ta Zama Firayi Minista

21:14 - July 14, 2016
Lambar Labari: 3480610
Bangaren kasa da kasa, muslmin kasar Birtniya sun fara nuna damuwa dangane da matsayin firayi minister da aka baiwa Theresa May saboda ra’ayin ‘yan mazan jiya da take da shi.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, bayan kwashe tsawon shekaru 26 da Margaret Thatcher ta za,a irayi minister a kasar Birtaniya a yau kuma Theresa May ta sake zama mace ta biyu a kan wannan matsayi.

David Cameron ya sanar da cewa zai yi murabus daga kan mukaminsa ne tun bayan da kasar ta kada kuri’ar raba gardama kan ficewa daga kungiyar tarayyar turai.

Wannan ya bayar da dama ga masu tsatsauran ra’atin yan mazana jiya domin su sake rike madafun iko a kasar, domin kuwa a halin yanzu kasar ta fice daga kungiyar tarayyar da suke kallonta a matsayin wani karfen kafa na hana su cimma manufofinsu.

Batun yaki da ta’addanci yana da cikin muhimamn batutuwa da suke a gaban majalisar dokokin kasar tun daga shekara ta 2015 har zuwa, yanzu kuma ko wace gwamnati za ta zo to dole ne ta dora daga nan.

Babban abin da musulmi suke fargaba a kansa dangane sake dawowar masu tsatsauran ra’ayin yan mazan jiya shi ne, yadda suke nuna kyama ga wasu bangarorii da bay an asalin kasar ba, musamman ma mabiya addinin muslunci wadanda akasarinsu yan kasashen ketare ne.

Bugu da kari kan hakan wannan mata tana daga cikin wadanda aka saba jin kalaman nuna kyama ga musulmi daga bakinta, wanda kuma hawanta kan matsayin firayi minister a kasar dole ne ya daga hankulan musulmi.

captcha