
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, Abdulhamid Dashti dan majalisar dokokin kasar Kuwait ya bayyana cewa, martanin wahbiyawa a kan hare-haren ta’addanci a kan kiristoci da ‘yan shi’a ya banbanta matuka.
Ya ce dukkanin larabawa sun yi Allah wadai da harin da aka kai birnin Nice na kasar Faransa ba tare da wani bata lokaci ba, amma a lokacin da aka kai harin Karada na kasar Iraki wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 300 sai suka yi gum da bakunansu.
Harin da aka kai a kan yankin yan shi’a na Karada da ke Iraki yay i sanadiyyar mtuwar mutane kimanin 290 da tare da jikkatar wasu fiye da 200 na daban.