IQNA

Kungiyar ISIS Ta Ce Ita Ke Da Alhakin Kaddamar Da Harin Birnin Nice Na Faransa

23:46 - July 16, 2016
Lambar Labari: 3480617
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar 'yan ta'adda ta ISIS ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kaddamar da harin birnin Nice na kasar Faransa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, Shafin yanar gizo na jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ya habarta cewa, shafin da 'yan ta'addan ISIS ke amfani da shi wajen saka sakonninsu a yanar gizo na Amaq ya fitar da wata sanarwa da ke cewa, kungiyar ta ISIS ce ke da alhakin kai harin an Nice.

Bayanin ya ce kungiar ta kai wannan hari domin daukar fansa kan hare-haren da ake kai mata a kasashen da take yin jihadi, sai a nasu bangaren jami'an tsaron kasar Faransa ba su uffan a kan wannan sanarwa ba, amma dai sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike.

Kasar Faransa dai ta kasance a sahun gaba tare da kasar Birtaniya gami da Amurka da sauran kawayen na larabawa wajen taimaka ma 'yan ta'adda.

3515424


captcha