
Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga shafin Express Tribune cewa, Jaridar Bishawur ta bayar da rahoto a shafinta na yanar gizo cewa, dubban musulmi a kasar Pakistan sun gudanar da jerin gwanon nea birane da yankuna daban-daban na kasar, domin nuna takaicinsu kan abin da yake faruwa kan musulmi a yankin Kashmir da ke karkashin India.
Daga cikin yankunan da aka gudanar da wannan jerin gwano a kasar ta Pakistan har da Bishawur da kuma Sawat gami da Kuita, da ma wasu sassa na kasar.
Masu gangamin da jerin gwanon sun yi Allawadai da kakkausar murya dangane da yadda al'ummomin duniya suka kasa tabuka komai domin dakatar da cin zarafin da ake yi wa bil adama a Kashmir, kamar kuma suka soki lamirin kasashen da ke raya cewa su ne shugabannin musulmi na duniya, yadda suka kauda kansu daga abin da yake faruwa na kisan kiyashin da India take yi wa musulmi.