Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta
cewa, Tashar talabijin ta Ala'alam ta bayar da rahoto daga birnin San'a
na kasar Yemen cewa, a yau jam'iyyun siyasa na kasar sun fitar da bayani na bai
daya, da ke yin tir da Allawadai da kakkausar murya, dangane da kisan kiyashin
da sojojin Saudiyya suka yi ma fararen hula a cikin daren Talata da ta gabata
kashe garin jiya Laraba.
Sojojin na Saudiyya tare da wasu mayakan da ta dauka haya daga kasashe daban-daban, sun afka kan kauyen Al-sarari a daren Talata, inda suka yi ta kashe fararen hula da suka hada da mata da kananan yara da tsoffi, inda a cikin daren suka kashe fararen hula 125, haka nan kuma sun kame wasu da dama sun yi awon gaba da su, wadanda ba a san yadda suka yi da su ba.
Jam'iyyun siyasar na Yemen suka ce kasashen ad ke da'awar kare hakkin bil adama a duniya da majalisar dinkin duniya sun ji kunya, ta yadda suka yi gum da bakunansu kan wannan mummunar ta'asa wadda ta yi hannun riga da 'yan adamtaka balantana addini.
Daga karshe jam'iyyun sun bukaci majalisar dinkin duniya da ta gaggauta gudanar da bincike kan wannan kisan kiyashi da Saudiyya ta jagoranta kan al'ummar kauyen Sarari a dake gungumar Ta'iz a cikin wannan mako.