IQNA

Hojjatol Islam Siddighi:

Muna Yin Kakkausar Suka Ga Kisan Kiyashin Da Saudiyya Take Wa Mutanen Yemen

23:33 - July 29, 2016
Lambar Labari: 3480658
Bnagaren siyasa, Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran a yau Juma'a Ayatullah Kazim Siddiqi yayi Allah wadai da irin kisan kiyashin da sojojin hadin gwiwan da Saudiyya take wa jagoranci suke yi wa al'ummar kasar Yemen wanda haka yayi hannun riga da dukkanin wata koyarwa ta Musulunci da kuma hakkokin bil'adama.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, Ayatullah Siddiqi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'ar a yau din a birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda yace irin wannan kisan gillan da Saudiyya take wa al'ummar Yemen wani kari ne na irin danyen aikin da take yi a duniyar musulmi.

Yayin da yake magana kan hare-haren da 'yan takfiriyya masu biyayya gakasar Saudiyya suka kai wani gari a kasar Yemen da tono kabarin daya daga cikin manyan malaman garin da kona gawarsa, na'ibin limanin na Tehran ya ce ko shakka babu wannan lamari yayi hannun riga da koyarwar musulunci.

Har ila yau kuma Ayatullah Siddiqi yayi kakkausar suka dangane da hare-haren ta'addancin baya-bayan nan da aka kai kasar Afghanistan da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 80 yana mai yin Allah wadai da halin ko in kula da MDD ta nuna kan hakan lamarin.

Dangane da abin da ke faruwa a kasar Bahrain ma, na'ibin limamin Juma'ar na Tehran yayi Allah wadai da irin zaluncin da mahukuntan kasar suke yi wa al'ummar kasar musamman matakan takurin da suka dauka a kan babban shehin malamin kasar Sheikh Isa Qasim.

Haka nan kuma malamin ya kira ga musulmi da su zama cikin fadaka dangane da yadda makiya suke t hankoron haifar da fitina ta bangancin mazhaba a tsakanin musulmi ta hanyar yin amfani da wasu kasashe da ke biyayya ga turawa ido rufe.

Ya ce idan msuulmi bas u yi hattara ba za su ci gaba da rarrabe kuma a lokaci guda hakan zai kara ma makiya karfi, ta yadda za su ci gaba da cin karensu babu bababka kan al’ummar musulmi kamar yadda muke ganin haka a halin yanza wasu kasashen larabawa.

3518581

captcha