IQNA

Bajen Kolin Farko Na Kur'ani Na Hadin Gwiwa Tsakanin Iran Da Senegal

23:31 - August 01, 2016
Lambar Labari: 3480667
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani baje kolin kur'ani na hadin gwiwa wanda shi ne na farko tsakanin Iran da Senegal a babban masallacin Dakar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na yanar gizo na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, a jiya fara gudanar da wani baje kolin kur'ani na hadin gwiwa wanda shi ne na farko tsakanin Iran da Senegal wanda ya hada cibiyoyin addini da makarantu na dukkanin bangarorin biyu.

Bayanin ya ce wannan baje koli ya samu halartar malamai da kuma jami'ai gami da masana daga dukkanin bangarorin biyu wadanda suka duba abubuwan da aka baje a wurin.

Daga cikina bubuwan da aka baje har da littafai da aka rubuta lokutan da suka gabata na addini, da kuma kwafin kur'anai da aka rubuta a kranoni daban-daban na tarihi.

Wadanda suka halarci wurin sun nuna gamsuwa matuka dangane da abubuwan da aka baje, wadanda suka hada har da wasu kayan al'adu na addinin muslunci na kasashen biyu wadanda suke da tarihi a nahiyoyinsu ta fuskarv addini.

3519291

captcha