
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jaridar New York Times cewa, Kwamitin bincike kan kisan gillar Zaria a karshen shekarar da ta gabata ya zargi sojojin Nigeria ta kashe mutane 347 a lokacin da suka kai wa yan shi'a mabiya sheikh Ibrahim Zakzaky haria cibiyarsu da ke Zaria da kuma gidansa da ke anguwar Gellesu a Zaria.
Sojojin Nigeria wadanda suke tare da babban hafsan sojojin kasar Lieutenant General Tukur Yusuf Buratai sun zargi mabiya sheikh Ibrahim Zakzaky da tare hanyar shugaban nasu. Rahoton ya bukaci gwamnatin Nigeria ta zakulo sojojin da suka aikata kisan da kuma bisne wadanda aka kashen a wani kabarin gama gari don gurfana a gaban kuliya.
A halin yanzu dai Sheikh Ibrahim Zakzaky yana tsare a hannun jami'antsaron kasar tun watan Disambanda ya gabata ana kuma ganin ya rasa idansa guda a lokacin da sojojin suka kama shi.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama a duniya sun bukaci a gudanar da bincike kan kisan na zaria don ladabtar da wadanda suke da hannu a cikin kisan.
Sojojin Nigeria dai sun dage kan cewa basu yi wani laifi ba a abin da ya faru a Zaria tsakaninsu da mabiyan kungiyar harka islamia.
Yanzu haka dai wannan batu yana gaban kotun manyan lafuka ta duniya, wadda ita ma take gudanar da nata binciken kan lamarin.