
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Lebanon ta Nhar Aljadid cewa, jami’an tsaron kasar Algeriya sun kame wani mutum mai cin mutuncin manzo (SAW) da keta alfarmar kur’ani mai tsarki ta yanar gizo.
Wannan mutum dai dan shekaru 46 da haihuwa yana zaune ne a garin Warsalan na kasar ta Algeriya, kuma yana amfani da hanyoyin sadarwa na yanar gizo ne wajen isar da sakonsa.
Daga cikin abin da yake yi har da tura sakonni na bayyana kur’ani mai tsarki a matsayin littafi maras kima, kamar yadda kuma yake yin kamalai na batunci ga manzon (SAW).
Baya ga hakan kuma wannan mutum yana bayyana mzo a matsayin mutumin da ke da dangantaka da ayyukan ta’addanci, inda yake bayyana cewa a lokacin rayuwarsa ya kasha mutane fiye da miliyan daya.
Kamar yadda kuma ya rika sukar juyin da al’ummar kasar suka yi inda suka kori yan mulkin mallakar kasar faransa da suka mamaye kasar tun shekarun da suka gabata.
Jami’an tsaro sun bi diddinsa tare da gano mabiyarsa, inda suka samu nasarar cafke shi da kuma mika shi ga bangaren shari’a, inda zai gurfana domin fuskantar hukunci.