IQNA

Za A Fara Shari'ar Masu Hannu A Fadowar Karfe A Kan Mahajjata

23:39 - August 05, 2016
Lambar Labari: 3480680
Bangaren kasa da kasa, za a fara shari'ar mutane 13 da suke da hannu a fadowar wani katafaren karfe a cikin dakin Ka'aba a ikin hajjin shekarar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran Kur'ani na Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin Shafaqna cewa, ana shirin fara shari'ar mutanen da suke da hannu a fadowar wani katafaren karfe a cikin dakin Ka'aba a ikin hajjin bara, duk kuwa da cewa wasu ab za su samu damar halartar wurin ba saboda raunuka da suka samu kuma alkalai 3 ne kawai za su yi shari'ar.

Bayanin yace dukaknin mutanen ana zarginsu da sakacia cikin ayyukan da suka jawo fadowar karfen wanda ya kashe mutane da dama, duk kuwa da cewa ana gudanar da binciken nea cikin sirri, kamar yadda ita shari'ar za a gudanar da ita ne a cikin sirri.

Tun bayan faruwar wannan lamari mahukuntan masarautar Saudiyya sun ce kamfanin zai biya diyyar dukaknin mutanen da aka kashe acikin dakin ka'abah suna dawafi, amma dai har yanzu shiri ba iya koda mutum day aba.

Mutane 107 suka rasa rayukansu daga cikin masu gudanar da ayyukan hajji a shekarar bara sakamakon fadowar karfen da ake yin aiki da shia lokacin da mutane suke dawafi, haka nan kuma an jikkata wasu 238 na daban.

3520191

captcha