IQNA

Yahudawa Da Kiristoci Sun Yi Allawadai Da Kisan Limamin New York

17:52 - August 15, 2016
Lambar Labari: 3480712
Bangaren kasa da kasa, wasu mabiya addinan kiristanci da yahudanci a Amurka sunfitar da bayanin yin Allawadai da kisan limamanin masallacin furkan da ke birnin New York.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Patch cewa, a jiya wasu mabiya addinan kiristanci da yahudanci a Amurka sunfitar da bayanin yin Allawadai da kisan limamanin masallacin furkan da ke birnin New York a lokacin da wani dan bindiga ya kai masu hari da bindiga,kisan cibiyoyi 120 na addini suka yi Allawadai da shi.

Sai dai anasu bangaren jamai'an 'yan sanda a birnin New York na kasar Amurka sun sanar da cewa, sun kame mutumin da ake zargin cewa shi ne ya yi wa limamin masallacin New York kisan gilla.

Tashar talabijin ta kasar Amurka ta bayar da rahoton cewa, a yau jami'an 'yan sanda na birnin New York sun kame mutumin wanda shi ne ake zargi da aikata wannan danyen aiki na kisan limamin masallacin Furkan da ke birnin na New York, kuma dukkanin alamun da shedun gani da ido suka bayar dangane da shi an same su a kansa.

A ranar Asabar da ta gabta ce dai aka harbe limamnin masallacin Furkan a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida bayan kammala sallar zuhur, yanzu haka dai 'yan sanda sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike a kan mutumin da suka kame da ake zarginsa da aikata wannan danyen aiki.

3522946

captcha