Bayanin kwararrun a fagen kare hakkin bil'adama ya yi kira ga gwamnatin Bahrain din da ta saki mutane da ta kama saboda mazhabar su ko kuma saboda tofa albarkacin bakinsu.
Bayanin ya kuma ce; Yadda ake kame mutane da kuma kiransu domin yi musu tambayoyi da kuma tuhumar da ake yi wa malaman addini da dama, sun taka rawa wajen raunanar hake hakkin bil'adama.
Daga cikin abubuwan da bayanin ya yiishara da su, da akwai rusa babbar jam'iyyar adawa ta alwifaq da kuma hana kungiyoin addini da malamai bayyana ra'ayinsu.
A daya bangaren kuma amsu fafutuka sun bayyana ci gaba da kame mayna malamai masu tasiri a kasar da masarautar kama karya ke yi, ya nuna irin yanayin da sarakunan kasar ke ciki na kaduwa da kuam tsorata da tasirin malaman.
Bayanin ya ce masarautar Bahrain tana tafka babban kure, domin kuwa malaman da take kamawa su ne suke tausasa al'ummar kasar daga yin duk wani gagarumin bore da zai kifar da masarautar baki daya, kuma ci gaba da yin hakan zai gaggauta kawo karshen mulkin masarautar kama karya da turawan mulkin mallaka suka kafa a kasar.
A baya-bayan nan masarautar Bahrain ta kame manyan malamai da suka nuna rashin amincewarsu da matakin da ta dauka na janye izinin zam dan kasa daga kan babban malamin addini na kasar, malamin da fiye da rabin al'ummar kasar ke kallonsa a matsayin shugabansu an addini.