Babban abin da yahudawan suke son aiwatar dai shi ne ginma wani wuri da suke kira na ibada da kuma a inda masallacin Aqsa yake za su gina shi wanda zai ci mita murabba'I dubu 720, kamar yadda kuma a gefensa za su gina wuraren kasuwanci da shaguna.
Ta ci gaba da cewa yanzu wannan shirin ya samu amincewa daga ofishin magajin garin birnin Quds na yahudeawa, domin kuwa Isra'ila ba ta son ta aiwatar da hakan da kanta kai tsaye, sai dai ta fake da wasu masu tsatsauran ra'ayi a kan cewa cewa su ne suka da shirin kuma tana goyon baya.
Yahudawan sun son aiwatar da wannan shiri ne a cikin shekaru uku masu zuwa, kuma shirin yana samun goyon bayan sauran yahudawa masu tsatsauran ra'ayi, daga cikin Isra'ila da ma wasu kasashe da suke zaune.
Kungiyar ta ce tana kira ga sauran musulmi larabawa da kiristoci da ma duk wani mai lamiri daga cikin mutane, da kuna giyar UNESCO da su mike domin tunkarar wannan mummunan shiri na yahudawan sahyuniya.