IQNA

Limamin Mauritaniya Ya Hudubar Idi Irin Ta Muftin Saudiyyah

15:56 - September 15, 2016
Lambar Labari: 3480782
Bangaren kasa da kasa, babban malamin kasar Mauritaniya ya yi hudubar idi daidai da irin babban mai bayar da fatawa na kasar saudiyya kan hadarin da ya kira safawiyawa.
Kamfanin dillancin labaran kur’an na iqna ya habrta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, Ahmad wuld Almurabit Habib Rahman ya yi hudubar sallar a wannan shekara daidai da irin da mai hudubar Saudiyyah, inda ya bayyana damuwa dangane da abin da ya kira hadarin akidar shi’a a cikin kasar Mauritaniya.

Malamin ya karanta wannan hduba n a dadai okacin da yake gabatar da hudubar salar idi ta wannan shekara, inda y ace babban abin da yake tunkaro yana da matukar hadari, shi ne zuwan fahimta irin ta mazhabar shi’a a tsakanin al’ummar kasar Mauritaniya.

Wannan dais hi ne kaon farko da aka taba jin haka daga bakin wannan malami a hudubar idi, lamarin da wasu danganta shi da abin da ya faru na sayen was daga cikin malamai da mahukuntan kasar Saudiyya suka yi domin biyan bukatunsu da sunan addini.

Kasashen Arka na daga cikin kasashen da aka bayar da rn kwangilata yada akidar rarraba kan al’ummar muuslmi da saa musu kiyayya da wani bangare na musulmi domin cimma burin a siyasa da kuma kare manuofin yaduwan sahyuniya.

Dubban mtane ne dai suka halarci sallar idin da malamin ya karanta wannan huduba, da suka hada shugaban kasar da kuma wasu daga ckin manyan ministoci da jami’an gwamnati, wanda hakan ya sanya hudubar ta bar baya da kura.

Masana masu ‘yanci a kasar dai sun yi kakkausa suka kan wannan mataki, inda suka bayyana hakan da cewa abin kunya ne kasar Mauritaniya ta siga cikin wannan rikicin domin kare manufar Al Saud kan wani bangare na al’ummar musulmi.

3530210


captcha