Benyamin Larence daya ne daga ckin mambobin majalisar kula da harkokin jama’a na zamantakewa akasar, ya bayyana cewa wannan babban abin kunya ne ga kasarsa.
Ya ce babu wani mutum da zai iya shafe samuwar wani dan kasa kowane irin addini yake yi domin kasar Afirka ta udu ab kasa ce da aka gina tsarinta kan addini ba.
Haka nan kuma ya yi kira ga masu kyamar musulunci da su sake tunani, domin kuwa irin wannan akida ba ta da wurin zama a cikin wannan kasa, domin duk dan kasa yana da hakki ya yi addinin da yake so ba tare da wata tsangwama ba.
Masu aida kiyayya da musulunci a kasar dai sun rika yin zane a kan bangaye a rana idin babbar salla suna aibanta musulmi da musulci, tare da yin kalaman batunc a kansu, da kuma bayyana su a matsayi kaskantatun mutane da ba yan kasa ba.