Khalid Aljashami shi ne shugaban kwamitin ayyukan tsaro na lardin Najaf ya bayyana cewa, suna cikin shiri domin tabatar da cewa an bayar da kariya ga rayuka da dkiyoyin jama’a masu ziyara a ranar Ghadir a wannan birni mai alfarma.
Ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai dubban jami’an tsaro da suka fara gudanar da ayyukansu a ciki da wajen birnin, da hakan ya hada da girke kayan aiki na bincike da kuma makamai na tsaro, domin tunkarar barazanar yan ta’adda a kowane lokacia wannan wuri mai tsarki.
Kamar yadda kuma ya yi ishara da cewa wannan aiki dakarun tsaro na lardin ne suka shirya shi, amma kuma sauran larduna da ke makwabtaka da Najaf Ashraf sun bayyana shirinsu na shiga cikin wannan aiki domin tabbatar da tsaro a birnin a yayin tarukan masu zuwa.
Aljshami ya kara da cewa yanzu haka sun fara gudanar da bincike na ababen hawa da ke kai komo a yakin baki daya, inda za a hana dukkanin abubuwan hawa shiga cikin birnin Najaf daga kilo mitoci a wajen birnin, kamar yadda za a rufe dukkanin hanyoyin shiga cikin birnin sai da ta hanyar mafi dadewa da ke isa hubbare mai tsarki.