Bayanin ya ce ko shakka babu irin matakan da wasu suke dauka na nuna yama ga mabiya addinin mulunci a wasu daga cikin kasashen nahiyar ya yi hannun riga da dukkanin kaidoji da dokoki na kungiyar.
A kan hakan ta yi kira da a dauki kwararan matakai na ganin an sa kafar wando daya da masu ni kiyayya da kyama ga mabiya addinin musulunci domin tabbatar da adalci a tsakanin dukkanin al’ummomin nahiyar dama yan adam baki daya.
Tun bayan bullar kungiyoyi masu kyamar muslunci a cikin wasu daga cikin kasashen nahiyar turai, ake samun masu tsananin kyamar addin da kuma musulmi msamman a manyan kasashen.
Daga cikin hanyoyin da ake nuna ma musulmi kyama a cikin kasashen turai har da rashin daukarsua makarantu ko wuraren ayyuka, kamar yadda kuma ake mayar da su saniyyar warea cikin wasu lamurra na zamantaewa, wada ya yi hannun riga hakkokin dan adam.