IQNA

An Gama Gasar Kur’ani Ta Rasha / Wakilin Iran Ya Zo Na Hudu

11:53 - September 26, 2016
Lambar Labari: 3480806
Bangaren kasa da kasa, an kammala gasar karatu da hardar kur’ani mia tsarki ta duniya a birnin Moscow na kasar Rasha.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta daga birnin Moscow cewa an kawo karshen gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya, inda Mahdi Sa’id ya sau matsayi na hudu a gasar kamar yadda Ustaz Abbas ya fada.

Malayzia, Yemen, Bahrain su ne suka zo a matsayi na daya, na biyu da uku, yayin da wakilin Iraki ya zo matsayi na biyar.

Reza Malki shi ne shugaban karamin ofoshin jakadancin kasar Iran a Moscow ya halarci wurin taron rufe gasar.

Kasashe 28 ne dai suka tura wakilansu a wannan gasa, inda suka kara da juna a bangarorin da aka gudanar da gasar a kansu.

Ustaz Abbas limamin Juma’a kuma daya daga cikin wadanda suka shirya gasar y ace, alkalan da suka jagoranci wannan gasa dai sun fito ne daga kasashen Morocco, Bahrain Turkiya da kuma Rasha.

An dai shirya wannan gasa ne tare da hain gwiwa tsakanin ofishin babban mai bayar da fatawa da kuma ofishin magajin garin birnin Moscow, tun a ranar farko ne dai wakilin Iran ya fara gudanar da karatunsa.

3532958


captcha