IQNA

An Haramta Harkar Muslunci A Najeriya

22:29 - October 08, 2016
1
Lambar Labari: 3480835
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da murkushe dukkanin ayyukan da harkar muslucni take gudanarwa a Najeriya a yau gwamnatin jahar Kaduna ta haramta ayyukan kungiyar.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga Press TV cewa, rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin kasar ta haramta dukkanin ayyukan kungiyar harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kadunan Malam Nasiru El-Rufai wato Samuel Aruwan ya sanya wa hannu ya ce gwamnatin ta haramta ayyukan kungiyar ta harkar Musuluncin a jihar bisa saboda karfin da tsarin mulki ya ba ta na tabbatar da tsaro da bin doka da oda a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa dokar haramcin wacce za ta fara aiki a yau din nan Juma'a ta tanadi daurin na shekaru bakwai ko kuma cin tara ko kuma duka biyun kan duk wanda aka samu ya karya wannan dokar da kuma gudanar da ayyukansa da sunan kungiyar.

Fitar da wannan dokar dai ta biyo bayan rikicin da ya faru ne a shekarar da ta gabata tsakanin sojojin Nijeriya da 'yan kungiyar ta IMN a garin Zariya inda sojojin Nijeriyan suka kashe daruruwan 'yan kungiyar saboda zargin cewa sun tsare wa babban hafsan hafsoshin sojojin Nijeriyan Janar Yusuf Tukur Brutai.

Sai dai a nata bangaren kungiyar ta 'yan Shi'a ta ce haramcin da kaka yi mata ya saba ka'ida.

Mai magana da yawun kungiyar Malam Ibrahim Musa ya ce za za su kaluabalanci wannan mataki na gwamnatin ta Kaduna.

Muna Allah wadai da wannan matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka, ba mu yarda da shi ba, za mu kalubalance shi ta dukkan hanyar da ta dace inshaallahu. inji Ibrahim Musa.

Amma ya ce matakin bai basu mamaki ba, ganin irin take-taken hukumomin na Najeriya dangane da kungiyar.

Kakakin na 'yan shi'a yace duk abin da su ke yi bai saba dokokin Najeriaya ba.

Daruruwan mutane ne suka mutu lokacin da sojoji suka afka mabiya mazhabar shi'a a watan Disamba 2015 bayan sojin sun yi zargin cewa 'yan Shi'a sun yi yunkurin halaka shugabansu, Laftanar Janar Yusuf Buratai.

Sai dai 'yan kungiyar sun musanta zargin, suna masu cewa sojoji sun kashe dubban mabiyansu ba tare da wata hujja ba, kuma suna ci gaba da boye lamarin har yanzu, wanda in gaskiya ne abin da suka fada sais u nuna wa duniya abin da suka aikata.

Hukumomi na tsare da Shugaban kungiyar Sheikh Ibraheem Zakzaky tun watan Disamba.

Kungiyar na da mabiya a sassan Najeriya da dama, amma wannan mataki zai yi aiki ne a jihar Kaduna kawai, inda nan ne hedikwatar ta 'yan Shi'a a kasar take.

Gwamnatin ta ce wannan mataki, wanda ya fara aiki a ranar Juma'a, ba a dauke shi ba ne domin hana mutane gudanar da addininsu kamar yadda dokar kasa ta basu dama.

Sai dai ta ce wannan dama tana da iyaka ta yadda ba za a amince ta tauye wa wasu hakkinsu ba.

3536361


Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
acigaba da hakuri haka harka tagada amma idan suna jida karrfi mulji zasu gama said kuma muga tacewa free sayyid
captcha