IQNA

Yunkurin Imam Hussain (AS) Shi Ne Misalin Kyakkyawar Bishiya / Al Saud Mabarnata Ne

22:30 - October 15, 2016
Lambar Labari: 3480857
Bangaren siyasa, Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Khatami limamin da ya jagoranci sallar Jumma'a a birnin Tehran a yau, ya ce Amurca da Britania sune a gaba gaba wajen goyon bayan ta'asan da Saudia da kawayenta suke aikatwa a Yemen.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarat cewa, , Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana Imam Hussain (AS) da kuma mikewar da ya yi a matsatin babban abin koyi ga dukaknin yan adam masu bukatar rayuwa a cikin yanci.

Haka ann kuma ya bayyana batun Imam Hussain (AS) da cewa lamari ne da ya shafi yan adamtaka, domin kuwa Imam ya tseratar da addini ne da yan adamtaka a lokaci guda.

Limamin ya yi Allah wadai da mummunan harin da gwamnatin kasar Saudia da kawayenta suka kai kan wani zauren da ake zaman makoki a birnin San'a na kasar Yemen a ranar Asabar takwas ga watan da muke ciki.

Rahotannin sun bayyana cewa a lokaci guda jiragen yakin kasar Saudia sun saki boma bomai masu nauyin kilogram dari takwas, sun mutanen da suke zaman makokin mutiwar mahaifin ministan cikin goda na kasar ta Yemen. Inda suka kashe mutan dari da arbain a lokaci suka suka kuma jikata wasu dari biyar da ashirin da biyar.

Aya. Ya yi All...wadai da shirin da kasashen duniya suka yi a kan wannan ta'asar, musamman kungiyoyin kare hakkin bil'adama da kuma Majalisar Dinkin duniya. Malamin ya kuma yi fatar za'a samat da majalisar dinkin duniya da take dinke duniyan da gaske ba irin wacce muke da ita yanzu ba.

Har'ila yau malamin ya yi fatan faduwar daular saudia karkashin ikon dangin Ali saudia mahukuntan kasar a halin yanzu sanadiyar ayyukan ta'addanci da suke aikatawa a kasashen duniaya daban daban.

3537565


captcha