Bayanin ya ce daukar wannan mataki yana a matsayin karfafa kyamar musulmi a cikin kasashen nahiyar turai, musamman kasar Italia, wadda ake kallonta a matsayin kasar da take kare hakkokin addinai.
Hakan ya sanya babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar fitar sanarwar yin Allawadai da daukar wannan mataki da mahukuntan kasar ta Italia suka yi, tare da yin kira da bude masallatai da kuma cibiyoyin musulmi da aka rufe a birnin Rom.
Mahukuntanan Italia dai sun ce sun dauki wannan mataki ne saboda dalilaina tsaro, musamman ganin cewa wadannan masallatai da kuam cibiyoyi suna yada akidar tsatsauran ra’ayi da kuma kin duk wani wanda ba musulmi ba, wanda hakan ya saba wa dokokin kasar.