Kamfanin dillancin labaran
kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo
na New Bury Taday cewa, a raar Juma'a da ta gabata mabiya addinin kirista daga
majami'ar birnin sun je masallacin Juma'a, kamar yadda su ma musulmi sun je
majami'a sun zauna a lokacin kiristoci ke ibadarsu.
Poul Covan shi ne shugaban majami'ar Cent George da ke birnin wadda tana daya daga cikin manyan majami'un kistoci a kasar Birtaniya, ya ziyarci masallacin Juma'a a lokacin sallar Juma'a kuma an yi sallar tare da shi.
Covan ya ce akwai abubuwa da dama da suke faruwa a duniya wadanada suke jawo tsoro da rashin yarda da juna, wadanda ya kamata su kawo karshe, domin musulmi da kiristoci ba abokan gaba ba ne, dukkaninsu mabiya addinai ne da aka safkar daga sama.
Ya ce za su ci gaba da yin kokari domin ganin an samu kyakyawar dangata tsakanin kiristoci da musulmi, ta yadda kiristocin da ke tsoron musulmi ko suke yi musu wani kallo su gane cewa ba haka musulmi suke ba.
Babban malamin kiristan ya ce tun bayan kisan da aka yi wa malamin kirista a Faransa a kwanakin baya, wasu kiristoci a kasashen turai sun dauki karan tsana sun dora kan msuulmi, alhali wadanda suka aikata wannan danyen aiki ba suna wakiltar dukkanin musulmi ba ne, bil hasali ma musulmin duniya sun yi Allawadai da hakan.