IQNA

20:32 - November 06, 2016
Lambar Labari: 3480914
Bangaren kasa da kasa, harin ta'addanci ya yi sanadiyyar yin shahada da kuma jikkatar mutane da dama a Samirra.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin alalam cewa, bisa ga rahoton Saumaria News a yau an kai harin ta'addanci da bama-bamao na kunar bakin wake a Samirra, wanda ya yi sanadiyyar shahadar wasu masu ziyara da suka hada da Iraniyawa.

Wakilin hukumar kula da ayyukan hajji da ziyara ta kasar ya tabbatar da shahadar Iraniyaw amasu ziyara guda 10 sakamakon harin na yau.

Daneshyar ya ce; dukkanin Iraniyawan sun safka daga cikin motar bas da take dauke da su a wurin ajiye motoci da ke wrin, kafin shiga wurin ziyara, inda dan ta'[addan da ya kai harin ya zoa cikin motar daukar marassa lafiya, nan take ya tarwatsa kansa.

Jami'an tsaro sun isa wurin ba da jimawa ba, inda suka killace wurin baki daya, tare da shiga gudanar da bincike kan lamarin, tare da hana zirga-zirgar jama'a, domin tsoron kada yan ta'addan su yi amfani da hakan wajen tayar da wasu bama-bamn.

Wani rahoton kuma yana cewa an kai wani harin ta'addanci a kusa da hubbaren Imamain, inda a nan ma mutane 10 suka yi shahada wasu kimanin 30 kuma suka samu munan raunuka.

Kamar yadda kuma wani labarin ke cewa a yau ma 'yan ta'adda sun kasha mutane a wani wurin bincike kafin shiga birnin Tikrit, inda a nan ma mutane da dama suka mutu tare da jikkata.

3543800


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، Samirra ، Iraki ، Iran ، shahada ، Imamain ، Tikrit
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: