IQNA

Mai Fatawa Na Sunna A Iraki:
23:42 - November 07, 2016
Lambar Labari: 3480916
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Mahdi Sumaida’i babban malamin sunna a Iraki ya bayyana cewa, malaman ahlu sunna na gaskiya ba su da wata alaka da ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, an bude babban taron tattaunawa na musulmi da kirista a karo na hudu tare da halartar masana daga sassa na duniya.

Sheikh Mahdi Sumaida’i wanda shi ne babban malamin ahlu sunna na kasar Iraki mai bayar da fatawa, ya bayyana cewa dukkanin ahlu sunna na gaskiya ba su tare da ‘yan ta’addan takfiriyyah, kuma ba su goyon bayansu, kuma duk wanda ya yi hakan hakia baya daga cikinsu.

Ya ci gaba da cewa yan ta’addan takfiriyya basu bar kowa ba hatta ma yan snna, domin kuwa shi kansa sai biyu yna tsallake rijiya ta baya sakmakon hare-haren kunar bakin wake da aka kai a kansa, amma Allah yana tseratar da shi.

Dangane da gwamnatocin da suke daukar nauyin ta’addan da sunan suna kare sunna ya ce sun tafka babban laifi, wanda Allah madaukakin sarki zai kama su a kansa, domin suna kashe musulmi sunna da shi’a da ma wadanda ba msuulmi ba, duk da sunan suna taimakon jihadia tafarkin sunna.

Daga karshe ya jaddada wajabcin hada kai tsakanin msuulmi baki daya domin fuskantar kalu balee da ke a gabansu, kamar yadda ya yi kira da a ci gaba da kara bunkasa alaka da mabiya addinin kirista domin kara samun fahimta a tsakaninsu da msuulmi a duniya baki daya.

A bangare guda kuma wasu daga cikin baki mabiya addinin kirista da suka halarci taron sun bayyana jin dadinsu matuka dangane da yadda wannan taro yake gudana, da kuma yadda aka nuna msu kulawa.

Shi ma anasa bangaren Cardinal Archbishop John Onaiyekan babban malamin addinin kirista daga tarayyar najeriya da yake halartar taron a birnin Tehran ya bayyana cewa, hakaika zaman lafiya shi ne mafi muhimmanci a cikin dukkanin lamurra da suka shafi rayuwar al’ummomi, kuma hakan zai samu ne ta hanyar fahimtar juna da girmama juna, wanda kuma gudanar da irin wadannan taruka za su taimaka matuka wajen ganin an cimma wannan buri da aka sanya a gaba.

3544007


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، fatawa ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: