IQNA

20:19 - November 09, 2016
Lambar Labari: 3480923
Bangaren kasa da kasa, an kammala babban taro na kasa da kasa kan karfafa alaka tsakanin manyan addinai na duniya guda biyu musulunci da kiristanci.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya nakalto daga shafin hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, a yau an kammala babban taro na kasa da kasa kan karfafa alaka tsakanin manyan addinai na duniya guda biyu musulunci da kiristanci tare da halartar masana daga kasashen duniya daban-daban a birnin Tehran.

Abu Zar Ibrahimi Torkman shugaban cibiyar yada al’adun mulsunci da kuma Ayatollah Taskhiri mai baiwa jagora shawara kan harkokin addini na kasa da kasa, da kuma Ayatollah Sayyid Mustafa Muhaqqiq Damad, da kuma Allamah Mahdi Mahdi Sumaida’i duk sauna daga cikin wadsanda suka halarci taron.

Masana da malamai na bangarorin kiristanci da kuma addinin muslunci da suka hada shi’a da sunna daga kasashen duniya sun halarci taron, da suka hada da kasashen Iran, Iraki, Lebanon, Nigeria, Switzerland, Italia, Vatican, India, Faransa, Birtaniya, Hong Kong da sauransu.

Mahalarta taron sun gabatar da jawabai da kasidun kan wajabcin karfafa alaka tsakanin manyan addinai na duniya, domin samun zaman lafiya da fahimtar juna, wanda shi ne abin da kowa yake bukata a halin yanzu a duniya.

Babban malamin addinin muslunci kuma babban mai bayar da fatawa na Ahlu-sunnah a Iraki Sheikh Allamah Mahdi Al-sumaida'i, ya fadi a gaban taron cewa, 'yan ta'addan da ke kashe bil adama da sunan abin da suke kira jihadi ko sunna abin da suke aikatawa ba kawai ba shi da alaka da sunna ba ne, a'a ba shi da wata alaka ne ma da addinin muslunci, shehin malamin ya ce musulunci addini ne da ke karramawa tare da girmama dan adam.

Shi ma a nasa bangaren babban malamin addinin kirista Cardinal kuma Archbishop na babban birnin tarayyar Najeriya Abuja John Onaiyekan, wanda ya halarci babban taro na kasa da kasa kan karfafa dangantaka tsakanin mabiya addinan musulunci da kiristanci, wanda ya gudana a Tehran na kasar Iran, ya jaddada wajabcin ci gaba da kara karfafa fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin dukkanin al'ummomi da kuma mabiya addinai na duniya, musamman manyan addinai guda biyu musulunci da kiristanci, inda ya ce an samu bababn ci gaba ta wannan fuska a kasarsa.

3544679


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: