IQNA

22:39 - November 14, 2016
Lambar Labari: 3480939
Bangaren kasa da kasa, cibiyar muslunci ta Hamburg za ta gudanar da tarukan makokin goman karshen watan safar.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na cibiyar musulunci cewa, a goman karshen safar za a gudanar da tarukan makokin wafatin manzon Allah (SAW) da kuma shahadar Imam hassan Mujtaba (AS) da kuma Imam Ridha (AS) a wannan cibiya da ke Hamburg.

Bayanin y ace kwana daya kafin ranar arbain za a fara gudanar da wanann shiri na makokin har zuwa karshen watan safar, inda a kowace rana za a fara daga karfe 18 na yamma har zuwa dare.

Daga cikin muhimamn abubuwan da za a yi kuwa har da wa'azi da tunatarwa, gami da bayani kan matsayin wadannan manyan bayin Allah tsarkaka amincin Allah ya tabbata a gare su.

Haka nan kuma akwai shiri na musamman wanda ya kebanci kanan yara ne kawai, da ya hada da basu kissosi gami da koya mus wasu daga cikin abubuwa na addini a cikin wadannan kwanaki.

Ga wadanda suke son bin wannan shii ta hanyar yanar gizo, za asu iya binsa kai tsaye ta hanyar shafin yanar na wannan cibiya.

3545873


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، safar ، Hamburg ، makokin ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: