IQNA

22:52 - November 16, 2016
Lambar Labari: 3480944
Bangaren kasa da kasa, hukumomi a Iraki sun ce ya zuwa yanzu 'yan kasashen waje kimanin miliyan daya da rabi ne suka shiga cikin Iraki domin ziyarar arba'in na Imam Hussain (AS) a Karbala.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraki Sa'ad Ma'in ya fadi yau Laraba cewa, ya zuwa yanzu kimanin yan kasashen waje miliyan daya da rabi ne suka shiga cikin Iraki domin halartar tarukan ziyarar arba'in na Imam Hussain (AS).

Ya ce dukkanin wadanda suka shigo cikin Iraki akwai tsarin da aka na kula da su da tsaronsu har su isa Karbala, ya ce wasu sukan shiga cikin kasar ba bisa kaida ba, irin wadannan ana mayar da su zuwa kasashensu ba tare da bata lokaci ba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iraki ya ce dukkanin wadanda suka shigo ya zuwa yanzu sun shigo ne bisa kaida wadda take akan dokokin Iraki, kuma ya zuwa yanzu babu wata matsala da aka fuskanta dangane da shigowar bakin, wanda a kowace rana adadin yana karuwa ne da dubban daruruwa.

Dangane da batun tsaro kuma ya tabbatar da cewa an kammala dukkanin tsare-tsaren da suka kamata, domin tabbatar da cewa an kare rayukan jama'a masu gudanar da wannan taro na ziyarar arba'in, wanda ake sa ran a shekarar bana adadin masu ziyarar zai haura miliya goma sha biyar.

3546559


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، miliyan ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: